Capitol Hill: Shugabannin duniya da suka yi Allah-wadai da rikicin siyasar Amurka

Masu zanga-zanga a Amurka da ke goyon bayan Shugaban ƙasar mai barin gado, Donald Trump, sun afka cikin ginin Majalisar Tarayyar Amurka, inda suke nuna rashin goyon bayansu ga nasarar Joe Biden.

Sun afka ne a cikin majalisar yayin da majalisun biyu ke wani zama na haɗin gwiwa domin amincewa da zaɓen ƙasar da aka yi a Nuwambar bara. Hakan ya sa jami'ai da ke aiki a cikin majalisar suka ba ƴan majalisar shawara da su gudu su ɓoye su dakatar da muhawarar da suke yi.

Duka waɗannan abubuwan sun faru ne jim kaɗan bayan wani jawabi da Shugaba Trump ya yi a ranar inda ya buƙaci masu goyon bayansa su yi tattaki zuwa Majalisar Tarayyar Amurka domin yin zanga-zanga.

Tuni dai wasu daga cikin shugabanni a duniya suka fara mayar da martani kan wannan rikicin siyasar.

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa burin siyasa na wani bai kai a zubar da jinin wani ɗan ƙasa ba. Mista Jonathan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.

"Na sha maimata cewa babu burin wani ɗan siyasa da ya kai har a zubar da jinin wani ɗan ƙasa, a ko ina a faɗin duniya. Babu kwata-kwata. Na ƙara maimaita cewa ya fi alkhari mutum ya rasa mulki domin a samu zaman lfiya, bisa ya samu mulki da zai jawo rashin zaman lafiya," in ji shi.

Firaiministan Canada Justin Trudeau

Firaiministan Canada, Justin Trudeau ya bayyana cewa ƴan ƙasarsa sun damu matuƙa bisa abin da ya faru a Amurka.

"Ƴan Canada sun damu matuƙa sakamakon harin da aka kai wa Dimokraɗiyya a Amurka, ƙawarmu kuma maƙwafciyarmu.

"Rikici ba zai taɓa zama hanyar danne abin da mutane ke so ba. Dole ne a jaddada Dimokraɗiyya a Amurka - kuma za a yi," in ji shi.

Firaiministan Birtaniya, Boris Johnson

Firaiministan Birtaniya, Boris Johnson, ya bayyana cewa abin da ya faru a Amurka, abin kunya ne, inda ya ce ƙasar ce ya kamata a ce ta yi tsaye kan dimokraɗiyya.

"Abin kunya da dama ya faru a Majalisar Amurka. Amurka tambarin dimokraɗiyya ce a faɗin duniya, kuma yana da muhimmanci a ce an miƙa mulki cikin lumana da bin tsari," in ji shi.

Emmanuel Macron na Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ma ya yi Allah-wadai da lamarin da ya faru a majalisar Amurkan US Capitol.

"Abin da ya faru a Washington DC ba Amurkar ba ce," kamar yadda Macron ya faɗa a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Tuwitta tare da rubutun "Mun yarda da dimokraɗiyya."

"Mun yi amanna da ƙarfinmu a dimokraɗiyyarmu. Mun yi amanna da ƙarfinmu a dimokraɗiyyar Amurka."

Angela Merkel ta Jamus

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tun da fari ta ce ta ji matuƙar taƙaici bayan da ta ga hotunan yadda lamarin ya kasance,yayin da su ma sauran shugabannnin ƙasashen Turai suka yi tur da lamarin.

A Rasha kuwa, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ce ta ɗora laifin rikicin kan tsoffin tsarin dokokin zaɓe na Amurka da kuma kafafen yaɗa labaran ƙasar.

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bayyana cewa miƙa mulki cikin zaman lafiya shi ne muhimmin abu fiye da komai.

Firaiministan Indiya, Narendra Modi

"Na damu da na ga labarin rikicin da ke faruwa a Washington DC. Dole ne a ci gaba da yunƙurin miƙa mulki cikin lumana.

"Ba zai yiwu a lalata dimkokraɗiyya ba ta hanyar gudanar da zanga-zanga ba bisa ƙa'ida ba," in ji shi.