ISWAP ta saki bidiyon da ta nuna yadda ta kashe wasu mutum biyar a Najeriya

ISWAP

Asalin hoton, AFP

Kungiyar ISWAP ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda ta kashe wasu da ta ce kiristoci ne da ta kama kwanan nan a shiyar-arewa maso gabashin Najeriya.

An dai fitar da bidiyon a ranar Talata wato a daidai lokacin da Boko Haram bangaren Shekau suka kashe wasu mafarauta bakwai a jihar Borno tare da raunata wasu 19.

Bidiyon mai tsawon dakika 49 ya nuna mutane biyar dauke da bindigogi kuma rufe da fuskoki tsaye a bayan wasu mutanen biyar wadanda su kuma ke gurfane a gabansu.

An ji wani daya daga cikinsu na cewa za su kashe mazan biyar ne domin ramuwar gayya da kuma aikewa da sako ga Kiristocin Najeriya da ma sauran duniya baki daya.

Daga nan kuma sai suka hahharbe mutanen biyar a keya.

Da ma dai kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai wani hari a kauyen Garkida na jihar Adamawa ran 24 ga watannan a jajibirin Kirsimati.

Inda suka yi da'awar kashe sojoji bakwai da kuma kama wasu mutane biyar.

Ko a ranar 26 ga watan Disambar bara ma sai da IS din ta fitar da wani bidiyo makamancin wannan da ke nuna yadda ta kashe wasu kiristoci 11.

An dai saki bidiyon ne a jiya Talata ranar da ita kuma kungiyar Boko Haram ta kashe wasu mafarauta bakwai tare da raunata wasu sha tara a kusa da kauyen Kayamla na karamar hukumar jere ta jihar Borno.

Mafarautan wadanda a kwanan baya aka basu makamai da motoci domin farautar 'yan Boko Haram sun gamu da ajalinsu ne lokacin da motarsu ta taka wata nakiya da mayakan Boko Haram suka binne kan hanyar da suke bi.

Kisan mafarautan dai na zuwa ne kimanin makonni uku bayan kashe wasu manoma 43 a kusa da kauyen Zabarmari shi ma a yankin Karamar hukumar jeren ta jihar Borno - wani abu da ya jawo Allah-wadai har daga majalisar dinkin duniya.