Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zhang Zhan: China ta ɗaure ƴar jaridar da ta ba da rahoton ɓarkewar annobar korona a Wuhan
An yankewa wata 'yar jaridar kasar China da ta bayar da rahoto kan barkewar annobar cutar korona a birnin Wuhan hukuncin daurin shekara hudu.
An samu Zhang Zhan da laifin ''neman fitina da haifar da rudani'', hukuncin da ake yawan yanke wa masu fafutika.
An tsare tsohuwar lauyar mai shekaru 37 a cikin watan Mayu, kuma ta shafe watanni da dama tana yajin cin abinci. Lauyoyinta sun ce yanzu ba ta da cikakkiyar lafiya.
Ms Zhang daya daga cikin sauran 'yan jaridun kasar da dama da suka fada cikin gagarumar matsala ce saboda bayar da rahoton da suka yi kan birnin Wuhan.
Babu 'yancin kafafen yada labarai a kasar ta China kuma an san mahukuntan da sa kafar wando daya da masu fafutika da masu kwarmata bayanai, da ake yi wa kallon masu yin kafar angulu wa kokarin da gwamnati ke yi kan annobar.
"Zhang Zhan ta shiga damuwa. Lokacin da aka bayyana sakamakon hukuncin da aka yanke mata,'' daya daga cikin lauyoyinta Ren Quanniu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mr Ren ya kara da cewa mahaifiyar Ms Zhang wacce ke cikin kotun, ta yi ta rusa kuka a lokacin da aka bayyana sakamakon hukuncin.
'Ƴar taratsi'
A wata tattaunawa da aka nada a faifen bidiyo da wani kamfanin shirya fina-finai mai zaman kansa kafin a cafke ta, Ms Zhang ta ce ta yanke sahawarar zuwa birnin na Wuhan a cikin watan Fabrairu bayan karanta wani labari da wani mazaunin birnin ya wallafa a shafin sada zumunta game da yadda rayuwa take a birnin lokacin annobar.
Lokacin da ta ke can, ta fara yada abubuwan da ta gani a kan tituna da asibitoci kai tsaye da kuma a rubuce, duk kuwa da barazanar da hukumomi ke yi mata, kuma an yi ta yada rahotanninta a kafofin sada zumunta da dama.
Gamayyar kungiyar masu rajin kare hakkin bil adama na kasar China CHRD ta ce rahotannin nata sun kuma fito da yadda aka tsare sauran 'yan jaridun masu zaman kansu da kuma cin zarafin 'yan uwan wadanda ake tsare da su da suka bukaci a yi musu adalci.
"Me yiwuwa ina da zuciyar 'yan tawaye ….ina bayar da rahotannin gaskiyar abinda ke faruwa ne. Me yasa ba zan fadi gaskiya ba?" ta fada a wani bangare na hirar wacce BBC ta samu.
"Ba zan daina abin da nake yi ba saboda ba zai yiwu wannan kasa ta rika ci baya ba.''
Ms Zhang ta yi ɓatan dabo a ranar 14 ga watan Mayu, kamar yadda kungiyar ta CHRD ta bayyana.
Bayan shekara guda, an bayyana cewa 'yan sanda sun tsare ta a birnin Shanghai, mai nisan fiye da kilomita 640.
A farkon watan Nuwamba ne aka tuhume ta. An zarge ta da aikewa da ''bayanan karya ta hanyoyin sakon waya a rubuce, bidiyo da suka sauran kafafen yada labarai ta hanyar shafukan sada zumunta kamar su WeChat, Twitter da kuma YouTube".
An zarge ta da amincewa da tattaunawa da kafafan yada labaran kasashen waje da kuma ''yada labaran karya'' game da kwayar cutar ta korona a Wuhan.
Yanke mata hukuncin shekara hudu zuwa biyar ne aka yanke shawara a kai.
'Hukunci mai tsauri'
Domin nuna rashin jin dadi game da cafke ta da aka yi ….Ms Zhang ta shiga yajin cin abince inda aka bayyana cewa ta kamu da rashin lafiya.
A wata sanarwa, daya daga cikin lauyoyinta ya ce lokacin da ya ziyarce ta a farkon watan Disamba, ta shaida masa cewa ana tilasta mata cin abinci ta hanyar wani bututun cin abinci.
Ya kuma ce tana fama da ciwon kai, jiri da kuma ciwon ciki.
"Bayan takura mata har na tsawon sa'a 24 a kowace rana, sai ta bukaci taimako wajen zuwa ban daki, kana takan rika juyi kan gado yayin da take barci,'' in ji lauya Zhang Keke.
"Ta shiga damuwa tare da galabaita, kamar a ce kullum ranar azaba ce.''
Lauyan ya nemi izinin a dage sauraron karar saboda yanayin lafiyar Ms Zhang.
An taba tsare Ms Zhang a shekara ta 2019 kan nuna goyon bayan masu fafutika a Hong Kong.
Leo Lan, wani mai bincike da wayar da kan jama'a a gamayyar kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar China CHRD, ya ce hukuncin da aka yanke wa Ms Zhang na baya-bayan nan ya yi "tsauri".
"Hukuncin da aka yanke mata ya yi tsauri ne. Gwmnatin China ta dage ta ga cewa ta kawar da ita, ta kuma ci zarafin sauran 'yan kasar da ke kokarin bankado abin da ya faru a Wuhan," ya shaida wa BBC.
"Na damu game da makomar sauran 'yan kasar da ake tsare da su, wadanda su ma suka bayar da rahoto game da annobar.''
Sauran manema labarai 'yan kasar da dama da suka bayar da rahoto daga Wuhan kamar su - Li Zehua, Chen Qiushi da Fang Bin - suka yi batan dabo a farkon wannan shekarar.
Daga bisani ne sai aka ga Li ya fito, yana mai cewa an tilasta masa killace kansa, yayin da aka bayar da rahoton cewa Chen na zaune tare da iyalansa amma karkashin sa idon gwamnati.
Amma kuma har yanzu ba a san inda Fang Bin yake ba.