Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Indiya: Ɗan majalisar da ya saki matarsa saboda ta sauya jam'iyya
- Marubuci, Daga Geeta Pandey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
Auren wani ɗan majalisar dokoki a Indiya da matarsa da ya fi shekara 10 yana rawa bayan da ya aika mata saƙon sakinta sakamakon sauya jam'iyya da ta yi.
A ranar Talata ne Saumitra Khan na jihar Bengal da ke yammacin ƙasar na jam'iyyar Fira Minista Narendra Modi wato BJP, ya aika wa matarsa Sujata Mondal Khan saƙon saki, kwana guda bayan da ta sauya sheƙa zuwa jam'iyyar TMC.
Jihar West Bengal na shirye-shiryen yin zaɓukan majalisar dokoki nan da watanni kaɗan kuma za a fi fafatawa ne tsakanin jam'iyyun BJP da kuma TMC.
A wajen wani taron manema labarai a babban birnin jihar, Kolkata a ranar Litinin, Ms Mondal Khan ta sanar da matakinta na barin jam'iyyar BJP tare da bayyana dalilanta na yin hakan.
Ta ce jam'iyyar ba ta nuna mata girmamawa ko kaɗan, inda ta fi karɓar "baragurbin ƴan siyasa" daga jam'iyyun adawa tana fifita su fiye da ƴan jam'iyya na ainihi masu kishinta.
Sa'o'i kaɗan bayan nan sai ɗan majalisar ya kira wani taron gaggawa na manema labarai, inda Mista Khan mai shekara 40 cikin hawaye da takaici ya sanar da matakin da ya ɗauka na rabuwa da matarsa bayan shafe shekara 10 suna tare.
Ya umarce ta da ta daina amfani da sunansa Khan a gaban sunanta, inda ya ce ya sakar mata mara ta je ta cika dukkan muradunta na siyasa, kamar yadda kafar yada labran Press Trust ta ruwaito shi yana faɗa.
Daga nan sai ya zargi jam'iyyar TMC da rusa masa gida.
"TMC ta sace min mata, ta ƙwace min farin cikina da soyayyata," a cewarsa.
Wani tsohon dan jarida a birnin ya ce "wannan wani abin mamaki ne da muke gani a siyasa wanda a baya ba mu taɓa ganin irinsa ba," an yi ta sanya labarin rabuwar auren a gidajen talabijin kuma ya matuƙar ɗaukar hankalin mutane.
Tun taron da aka yi a ranar Litinin, manema labarai ke ta bin ma'auratan don yi musu tambayoyi kan rayuwarsu da kuma siyasarsu.
"Masoyiyata ce. Mata ce ta gari. Ina da rauni sosai idan aka zo batunta. Babu shakka abin ya taɓa ni sosai. Muna tare sama da shekara 10," in ji Mista Khan.
Ya kuma bayyana irin rawar da matarsa ta taka a nasarar da ya samu a zaben shekarar da ta gabata, an hana shi shiga mazaɓarsa saboda wata shari'a da ke da alaƙa da wani babban laifi, amma ita ta rika yakin neman zaɓe da a madadinsa, ta riƙa zuwa gida-gida tana neman a zaɓe shi, tana zuwa ƙauyuka tana kuma yi musu bayani.
"Amma wannan labarin ya zo karshe. Ba ni da wata alaƙa da ita ko kadan," kamar yadda ya ce "ni yanzu babu komai tsakani na da Sujata."
Ya kuma shaida wa wani dan jarida cewa ya rabu da matarsa ne saboda ikirarin da ya yi na cewa ba ta girmama jam'iyyar BJP "Mista Modi yana kiranta 'yar uwarsa. To kuma me take nema? Ya tambaya.
Misis Mondal Khan ita ma ta yi ta tattaunawa da 'yan jarida tana zargin mijinta da daina kula ta sama da wata 10.
"Harkokin siyasarsa ne kawai a gabansa. Ba shi da lokacina. Sama da watannin bai damu da ya tambaye ni ko na ci abinci ba ko kuma yaya na kwana," in ji ta.
Kuma ta zargi shugabannin jam'iyyar BJP "suna zuga" mijinta da kokarin sa shi ya "kawo karshen aurensu".
"Su wane ne suke mini bi-ta da ƙullin cewa Soumitra yana mini barazanar saki? Ta tambaya a yayin hira da wakilin jaridar Primetime.
Sauya shekar jam'iyyar siyasa ba wani bakon abu ba ne a Indiya. Bai bai wa Mista Khan mamaki ba - domin shi ma ya fara rayuwar siyasarsa ne a jam'iyyar Congress kafin daga bisani ya koma TMC a 2013 daga baya kuma ya koma BJP a watan Janairun 2019.
A Bengal, kamar yadda Mis Modela Khan ta buga misali, 'yan siyasa na kasa kamar mahaifi da dansa, ko kanin mahaifi, - wadanda suke goyon bayan jam'iyyu daban-daban "cikin farin ciki babu wanda ya ce musu su rabu".
"Wannan duka makircin BJP ne, suna ta cewa ya rabu da ni," kamar yadda ta shaida a wata tattaunawa.
"A ganina siyasa daban mu'amalar iyali daban, kuma bai kamata a riƙa haɗa su ba."