Saudiyya ta kama mutum 16 da fataucin miyagun kwayoyi

Hukumomin Saudiyya sun kama masu fataucin miyagun ƙwayoyi guda 16 da ke ayyukansu a babban birnin kasar, Riyadh da kuma birnin Jeddah.

Hukumar hana fataucin miyagun ƙwayoyi ta General Directorate of Narcotics Control ce ta kama mutanen yayin da suke ƙoƙarin shiga da ƙwayar amphetamine kusan kusan miliyan 20 cikin kasar.

Jaridar Saudi Gazzette ta ruwaito mai magana da yawun hukumar, Captain Muhammad Al-Najidi, yana cewa 10 daga cikinsu 'yan kasar ne, shida kuma 'yan kasashen waje.

"Tawagar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ta yi nasarar tarwatsa wani sansanin masu laifi a Riyadh da ya ƙunshi 'yan kasar har mutum biyar da suka ƙware wurin sayar da ƙwayoyi kuma an ƙwace jumullar ƙwayar amphetamine 9,878,500 daga hannunsu," in ji shi.

Al-Najidi ya ce an sake kama wasu mutum 10 a Jeddah, inda aka tarar da amphetamine guda 5,827,000 ƙunshe a cikin wasu kaya a gidansu.

A wani samamen na daban, an kama wani ɗan kasar waje a lokacin da yake yunƙurin shiga da amphetamine guda 3,228,323 a cikin wani ƙunshin kayan dankali a yankin Al-Haditha da ke kan iyakar ƙasar da Jordan.

Ƙasar Saudiyya na daga cikin ƙasashen duniya da ke da tsauri matuƙa wurin yanke hukunci idan aka samu mutum da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

Ƙasar ta yanke wa mutane da dama hukuncin kisa. Sai dai a wasu lokutan, ana samun wasu ɓata gari da ke saka wa maniyata aikin Umara ko Hajji ƙwayoyi a cikin kayansu.

Ko a kwanakin baya sai da 'yan Najeriya kusan mutum biyu wannan lamari ya faru da su, inda daga baya gwamnatin Najeriyar ta taimaka wurin ceto su bayan tabbatar da ba su da laifi.