Boko Haram ta ƙone gari ta kashe mutum 27 a Nijar

Ƙungiyar Boko Haram ta kai wani mummunan hari a yankin Diffa kudu maso gabashin Nijar inda ta kashe aƙalla mutum 27.

Ƙungiyar ta kuma ƙone ɗaruruwan gidaje da kasuwa da motoci a harin da ta kai da ta shafe sa'a uku a a ƙauyen Toumour a tsakanin daren Asabar zuwa Lahadi.

Mutane da dama ne aka ƙone bayan cinna wa gidajensu wuta, kuma da dama sun ɓata sun shiga daji.

An kai harin ne yayin da ƙasar ke shirin zaɓen ƙananan hukumomi a ranar Lahadi.

Bayanai sun ce tsakanin gida 800 zuwa 1,000 aka ƙone. Mayakan sun kuma kashe mutane bayan buɗe masu wuta.

Wani jami'i a yankin ya ce mayaƙan kimanin 70 ne suka abka wa garin na Toumour da yamma.

Kuma sun fara kai hari ne a gidan mai gari, wanda Allah ya ba shi sa'ar tserewa.

Jami'in ya ce kusan kashi 60 na gidajen garin aka ƙone.

Yankin Diffa na Nijar da ke makwabtaka da jihar Borno ta Najeriya ya sha fama da hare-haren Boko Haram, kuma bayanai sun ce mayakan sun ƙetara tafkin Chadi ne suka kai harin na ranar Asabar.