Ɗaliban Kankara: Zaratan 'yan sanda da sojoji sun shiga neman ɗaliban sakandaren Kankara

Har yanzu ba a gano ƙarin wasu daga cikin ɗaruruwan ɗaliban da ake zargi 'yan bindiga sun sace a makarantar sakandaren maza GSSS Ƙanƙara da ke jihar Katsina ta Najeirya ba kwana biyu bayan sace su.

Bayanai sun ce 'yan bindigar sun sace ɗaruruwan ɗalibai daga sakandaren ta Ƙanƙara yayin wani hari da suka kai ranar Juma'a da daddare.

Lamarin ya faru ne a yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jihar ta Katsina.

Wasu bayanai sun ce akwai ɗalibai fiye da 600 a yayin da aka kai harin, sai dai kakakin rundunar 'yan sandan Katsina DSP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa tuni aka gano ɗalibai fiye da 200.

Babban Sifeton 'yan Najeriya Mohammed Adamu ya bayar da umarnin aike wa da zaratan 'yan sanda waɗanda za su yi aiki da sojoji da wasu jami'an tsaro domin gano ɗaliban.

Sanarwar da mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya DCP Frank Mba ya fitar ranar Asabar ta ce "jami'an tsaron da aka aike sun haɗa da rundunar 'yan sanda ta musamman da 'yan sanda masu kai hari na musamman... waɗanda za su taimaka wa rundunar 'yan sandan Katsina wajen gudanar da bincike."

Ya ce shugaban 'yan sandan ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a dukkan makarantun sakandare da ke faɗin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gano maɓoyar 'yan bindigar kuma ta yi musayar wuta da su a wani daji.

'Damuwa da firgici'

Iyayen yaran da aka sace sun bayyana wa BBC irin mawuyacin halin da suka shiga tun da aka sace 'ya'yansu.

Mahaifin wasu ɗalibai biyu ya shaida mana cewa tun da lamarin ya faru suke cikin damuwa "domin duk lokacin da aka ce yaronka ya ɓata dole ka shiga damuwa, don gara ma a ce mutuwa ya yi."

Ya ce mahaifiyar yaran ta shiga damuwa sosai ko da yake sun fawwala komai ga Allah.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, wanda ya ziyarci makarantar ranar Asabar, ya bayar da umarnin rufe ɗaukacin makarantun sakandare na kwana da ke faɗin jihar.

Rahotanni sun ce jama'ar da wurin sun yi masa ihu yayin da ya yi yunƙurin yi wa iyayen yaran jawabi har sai da aka harba hayaƙi mai sa hawaye kafin tawagar gwamnan ta iya barin wurin.

BBC ta tuntuɓi Ibrahim Ahmad Katsina, mai bai wa gwamnan shawara kan harkar tsaro wanda ya tabbatar da ɗaukar matakin.

Ya ce hukumomi a jihar sun yanke shawarar ɗaukar matakin da gaggawa domin kwantar wa iyaye da su kansu ɗaliban hankali, da kuma tabbatar da cewa lamarin bai shafi wasu makarantun ba.

Ya ce kawo yanzu ana kan ƙoƙarin tantance adadin ɗaliban da aka sace yayin harin, da kuma waɗanda suka gudu zuwa gidajensu.

Bayanai sun ce har yanzu wasu iyaye suna harabar makarantar inda suke jiran ganin an dawo da 'ya'yansu.

Tun da farko rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar wa BBC kai harin amma ta ce ba ta da bayanai kan sace ɗaliban.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Gambo Isa, ya ce tuni aka gano ɗalibai fiye da 200 da suka tarwatse suka shiga cikin daji a lokacin da 'yan bindigar suka auka wa makarantar tasu.

Ya ƙara da cewa an yi ba-ta-kashi tsakanin 'yan bindigar da 'yan sanda lamarin da ya kai ga "harbin ɗan sanda ɗaya amma bai mutu ba."

Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da 'yan bindiga ke kai hare-hare, kuma lamarin ya ta'azzara a baya bayan nan.