Coronavirus Italy: Mutumin da ya yi tafiyar mako guda da ƙafa don huce haushin faɗa da matarsa

Wani mutumin Italiya ya fice gidansa domin ya huce bayan faɗa da matarsa - har ya yi tafiyan kilomita 450.

Italiyawa a kafofin sadarwa na intanet, har sun raɗa masa sunan wani fim "Forrest Gump" na wani jarumi a 1994 na Tom Hanks, wanda ya yi tafiyar dubban kilomita a sassan Amurka.

Ƴan sanda sun dakatar da shi daga tafiyar da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare a Fano, mako ɗaya bayan ya bar gidansa da ke yankin arewaci.

Mutumin, mai shekara 48 ƴan sanda sun ci tararsa fam 362 kan saɓa dokar hana fita.

Jaridar Resto del Carlino a yankin Bologna ce ta fara wallafa labarin, kuma nan take ya mamaye kafofin yaɗa labaran Italiya.

An samu mabambantan ra'ayi a kafofin sadarwa na intanet inda wasu suka kira mutumin jarumi tare da bayyana adawa da tarar da aka ci shi.

Wani ya ce kamata ya yi ma a karrama shi - amma ba a ci shi tara ba. Wani kuma ya jinjina masa na fita domin ya huce, maimakon haddasa rikici.

Mutumin ya ce "na zo nan da ƙafa, ban hau mota ba." ya kuma ce "kan hanya na haɗu da mutane da suka yi min tayin abinci da ruwa. Na gamsu amma na gaji," a cewarsa inda yake tafiyar kilomita 60 a rana.

Ƴan sanda sun same shi cikin sanyi da dare a kan babbar hanya.

Bayan duba katinsa na shaida, sun gano cewa matarsa ta bayar da sanarwar cewa ya ɓata. Nan take suka tuntuɓe ta kuma ta zo Fano domin ta karɓe shi.

Rahotanni daga Italiya ba su bayyana yadda ya fusata ba bayan cin shi tara.