Abdullahi Umar Ganduje: Abin da ya sa gwamnan Kano zai ɗaure iyayen da ke hana ƴaƴansu zuwa makaranta

Ganduje

Asalin hoton, PT

Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanya hannu a kan wata doka da ta tanadi hukuncin ɗauri a gidan yari ko kuma tara ga duk iyayen da aka samu da laifin ƙin sanya ƴaƴansu a makarantar boko.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanya wa dokar hannu a baya-bayan nan, abin da ke nufin cewa wajibi ne a kai kowanne yaro da shekarunsa suka isa zuwa makaranta, aji.

Kwamishina ilimi na jihar Muhammad Sanusi Sa'idu Kiru, ya shaida wa BBC cewa, nan gaba za a kafa kwamitoci a ƙananan hukumomi wanda zai ƙunshi masu ruwa da tsaki ciki har da masu unguwanni domin tabbatar da cewa yara na zuwa makaranta.

Kwamishinan ya ce: "Duk uban da aka samu ko wani ya karya wannan doka to tabbas za a ci shi tara, kuma tarar ta haɗa da idan laifin farko ne to za ayi gargaɗi a kan kada a sake sannan ya kai ɗansa makaranta".

Ya ce, "Idan kuwa mutum ya sake kwatanta wannan laifi na ƙin kai yaro ko yarinya makaranta, to za aci tarar naira dubu ashirin ko kuma zaman gidan yari na tsawon wata guda".

Muhammad Sanusi Sa'idu Kiru, ya ce idan kuwa aka samu masu ruwa da tsaki da suka hada masu unguwanni da malamai da ƙin bayyana iyayen da ba su kai yaransu makaranta ba, to za a ci tarar su naira dubu biyar ko zaman gidan yari na wata guda shi ma.

Tuni dai iyayen yara a jihar suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan doka ta tilasta kai ƴaƴa makaranta da gwamnatin jihar ta ɓullo dashi.

Wasu iyaye da BBC ta tattauna da su sun ce suna maraba da wannan mataki sai dai fatan Allah ya sa hakan ya ɗore, yayin da wasu kuma suka ce akwai gyara a wannan tsari kasancewar shi kansa ɓangaren ilimi a jihar na da nasa ƙalubalen.

Ƙarin bayani

Bayanai dai sun nuna cewa adadin yaran da suke zuwa makaranta a Kanon na ci gaba da ƙaruwa a dai-dai lokacin da fannin ilimi ke fama da tarin matsaloli ciki har da ƙarancin kayan aiki, sannan su kansu hukumomin jihar sun tabbatar da cewa akwai makarantun firamare da na sakandire da suka haura dubu uku da rufin gininsu ya ɗaye.

Sanna kuma ga wasu ginin ajujuwan da suka rushe waɗanda aka ƙiyasta cewa zasu laƙume kuɗi fiye da naira biliyan talatin wajen gyara su.

Kafin zuwan gwamnatin Ganduje, gwamnatin da ya gada dai tana da tsarin bayar da ilimi kyauta tun daga matakin firamare har zuwa makarantun gaba da sakandire.

Amma da gwamnatin Ganduje ta hau mulki sai ta soke wannan tsari abin da ya janyo ce-ce-ku-ce a wancan lokacin.