Cutar korona: Ma'aikatan lafiya na cikin mawuyacin hali a Kongo

Ma'aikatan lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun ce suna cikin mawuyacin hali a ƙoƙrinsu na shawo kan annobar korona da ke ci gaba da yaduwa a faɗin ƙsar.

Yanzu haka dai asibitoci a ƙasar na fama da matsalar rashn naurar taimakawa numfashi da akan sanyawa masu cutar korona a duk lokacin da suka buƙce ta.

Shugaban tawagar da ke jagorantar yadda kasar ke shawo kan cutar, Jean-Jacques Muyembe, ya ce yanzu haka cutar na sake yaɗuwa a zagaye na biyu, sannan halin da ake ciki ya yi matukar fin na baya muni.

Wasu rahotanni sun nuna cewa waɗanda suka kamu da cutar a wannan lokaci sun fi shiga mummunan yanayi fiye da da na baya.

Ya ce yawan yankewar wutar lantarki a Kinshasa babban birnin kasar na kawo cikas ga samar da iskar oxygen, ma'ana asibitoci galibi suna da karancin kayan aiki.

Zuwa yanzu dai an samu kusan mutane dubu goma sha uku-da dari biyar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Jamhuriyyar Dimukraɗiyyar Congo.

Cikin shekaru biyu da suka gabata, Jamhuriyyar Dimkoraɗiyyar Congo ta yi fama da annobar cutar ƙyanda mafi muni a duniya, wacce ta kashe fiye da yara 7,000.

Sannan ana kallon ƙsar a matsayin wadda cutar Ebola da aka yi fama da ita a nahiyar Afrika a baya-bayan nan tafi shafa, domin ta hallaka ɗaruruwan mutane a ƙasar, sannan akwai rahotannin da ke cewa har yanzu akwai sauranta a ƙasar.

Kusan mutane miliyan 22 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo na fuskantar matsalar karancin abinci kamar yadda wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi.

"Yawan mutanen da ke fuskantar matsalar karancin abinci ya ƙaru matuka daga miliyan 15.6 a shekarar 2019 zuwa miliyan 21.8," in ji Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya a cikin wani rahoto.

Kungiyar ta ce rikice-rikice da illar wannan annoba ta Covid-19, wacce ta yi tasiri ga farashin kayan abinci da na rayuwa, sun ta'azzara matsalar.