Mata a zaben Ghana: Ga biki babu zanin daurawa

A duk lokacin da ake zabe a musamman a kasashen Afrika mata na taka muhimmiyar wajen nema wa 'yan takara goyon bayan da kuma jefa musu kuri'a.

Sai dai ba kasafai ake samun mata na fitowa takara don su ma a zabensu ba. To ko yaya lamarin yake a kasar Ghana inda ake shirye-shiryen manyan zabuka a makon gobe?

Kamar a galibin kasashen, mata a Ghana su ne kusan rabin al'ummar kasar inda suka dauki fiye da kashi 49 cikin 100 na yawan jama'arta.

Haka ma a bisa alkaluman hukumar zaben kasar kashi 51 cikin 100 na wadanda suka yi rijista domin jefa kuri'a a wannan zaben na bana mata ne.

To amma idan aka zo wajen rikon mukamman siyasa matan kasar na baya kwarai; domin a halin yanzu kashi 13 cikin 100 ne kawai mata da ke majalisar dokokin kasar balle a matakin zartawa inda adadin bai kai haka ba.

Hakan dai na faruwa duk a cewar Zeinab Sallaw wakiliya a kwamitin zartarwa na kasa na jam'iyya mai mulki ta NPP, jam'iyyu na karfafawa matan gwaiwar su fito takara.

"Mace idan za ta tsaya takara jam'iyyar NPP kan ce ka da wanda ya yi takara da ita. Kuma kudin da ya kamata mai neman takara ya biya jam'iyya kan ce tun da mace ce a rage mata kashi 80 cikin 100 na kudin don mu mata mu samu shiga a dama da mu," in ji ta.

Ita ma dai Hajiya Rahmatu Saakib wakiliya a kwamitin kamfe na jam'iyyar Adawa ta NDC a jihar Ashanti ta ce ba a bar jam'iyyarsu a baya ba wajen bai wa mata damar shiga a dama da su a zabe.

Ta ce wannan ne ya sa dan takararsu na shugaban kasar ya zabo mace a zaman mataimakiyarsa.

To ko me ya kawo rashin shigar mata sosai a harkokin siyasar duk irin wadannan damammakin da ake ba su?

Bakunan duka wakilian manyan jam'iyyun biyu sun zo daya kan amsar wannan tambaya.

Sun bayyana dalilai da suka hada da na aure da kula da yara da aiki da rashin ilmi da kuma rashin kudin a zaman manya dalilan da ke yi wa mata a kasar Ghana tarnaki wajen tsayawa takara.

"Wata kuma na nan akwai ilmin akwai kudin amma tana jin tsoro domin shiga cikin jama'a ba abu ne mai sauki ba, ba kowa zai iya ba," in ji Rahmatu, wakiliya a kwamitin kamfe na jam'iyyar adawa ta NDC.

A halin yanzu dai da matan kasar ke da 'yan majalisar dokokin 36 daga cikin 275 wato kashi 13 bisa dari, Ghana ta samu ci gaba ta fuskar bai wa mata damar rike mukaman siyasa.

Domin wannan shi ne karo farko da adadinsu ya kai haka a majalisar tun bayan samun 'yancin kanta fiye da shekaru 60 da suka wuce.

Sai dai kuma masu sharhi na ganin har yanzu kasar na bayan ta wannan kokarin idan aka kwatanta da wasu kasashen na Afrika tsaranta kimanin 24 inda wakilcin mata a fagen siyasa ya kai kashi 20 cikin 100.