Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harbe-harben Lekki Toll Gate: Abin da ya faru zuwa yanzu a gaban kwamitin shari'a na gwamnatin Legas
Harbe-harbe a Najeriya yayin zanga-zangar da aka yi a watan jiya don nuna adawa da cin zalin 'yan sanda a Lekki da ke jihar Legas, babbar cibiyar kasuwanci a Najeriya ya haifar da tofin Allah-tsine a faɗin duniya.
Amma bayan batun cewar tabbas an buɗe wuta, akwai saɓani tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro kan haƙiƙanin abin da ya faru a daren.
Ana fatan cewa kwamitin binciken da aka kafa don bincikar abubuwan da suka faru a Lekki da kuma batun da ya shafi zaluncin yan sanda zai yi ƙarin haske, sai dai ba wannan ne batun ba har yanzu.
Wakilanmu sun kasance a wurin zanga-zangar ta Legas kuma wannan shi ne abin da ya gudana kawo yanzu:
Wanene ya nemi sojoji su je Lekki toll gate?
Kasancewar sojoji a wajen yayin zanga-zangar lumana ta jawo ce-ce-ku-ce sosai amma har yanzu ba a bayyana wanda ya ba da umarnin ba.
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya ayyana dokar hana fita a ranar 20 ga watan Oktoba don dakile tashin hankalin da ya barke a wasu sassan jihar yayin zanga-zangar adawa da cin zalin da ƴn sanda masu yaƙi da fashi da makami wato (Sars) ke yi.
'Yan sa'o'i kaɗan bayan da aka sanar da dokar hana zirga-zirgar, sojoji sun isa wajen da masu zanga-zangar #EndSars suka yi sansani na kwanaki.
Dangane da kasancewar sojoji, Mista Sanwo-Olu ya fada wa gidan talabijin na Arise TV ranar 22 ga Oktoba cewa ba shi da ikon neman sojoji a wurin zanga-zangar a matsayinsa na gwamnan jihar.
Sai dai su Sojojin, sun fadawa kwamitin da ke gudanar da binciken a ranar 14 ga Nuwamba cewa sun je wajen ne sakamakon gayyatar da gwamnan ya yi musu.
Birgediya-Janar Ahmed Taiwo ya ce gwamnan ya nemi sojoji su shiga lamarin ne saboda yadda ya gagari ƴan sanda.
A wani taro da aka yi a ranar 21 ga Nuwamba, wakilin sojoji a wajen taron ya ce aikinsu ba wai don su kawar da zanga-zangar ba ne face "tabbatar da zaman lafiya a hanyar Eti-Osa wato yankin da ke kusa da wajen da masu zanga-zangar suka taru. Har yanzu gwamnan bai maida martani ga sojoji ba.
Shin sojojin sunyi amfani da harsashi mai kisa?
Akwai dai zargin cewa sojoji da 'yan sanda sun harbi masu zanga-zangar da sauran mutanen da ke kusa. Amnesty International ta ce mutane 12 ne suka mutu.
A farkon zaman kwamitin, sojojin sun musanta kashe kowa kuma sun dage kan cewa sojojin da ke wajen sun yi ta yin harbi a sararin samaniya ne, inda masu zanga-zangar suka taru.
A ranar 21 ga Nuwamba, Brig-Gen Taiwo ya faɗa wa kwamitin cewa sojoji sun yi amfani da harsasai masu kisa don tarwatsa ƴan daba "waɗanda suka fake da zanga-zangar wajen tada yamutsi.
A lokacin da yake amsa tambayoyi, wakilin sojojin ya ce wasu 'yan banga sun jefi sojojin da ke sintiri a kusa da otal din Oriental, gab da Lekki toll gate, wanda ya kai ga soja daya ya samu raunuka.
Idan aka kawo mana hari da duwatsu, abin da kawai za mu a iya yi shi ne harbi.
Shin rahoton na BBC ya gaskata abin da sojojin Najeriya suka ce?
A zama daban-daban, da kuma wata sanarwa ga manema labarai, sojojin sun gabatar da rahoton BBC na harbe-harben na Lekki don tabbatar da matsayinsu na cewa sun yi harbi a sama ba ga masu zanga-zangar ba.
Wakiliyar BBC Pidgin Damilola Banjo a cikin rahoton nata, ta bayyana abin da ta gani ne kawai a wurin zanga-zangar inda take gabatar da rahoto kai tsaye.
Banjo, wadda ta bar wurin misalin minti 25 bayan sojojin sun iso, ta ce:"Kafin mu bar wurin, su [sojoji] suna ta harbi a iska kuma yayin da muke kokarin neman wani abin kariya, sai na ga wani saurayi da alama yana ta faman numfashi."
''Ina ganin abin da dole ya haifar masa da hakan shine ya firgita da harbe-harben da sojoji ke yi ne, ba shakka yanayin ya ƙazanta''.
"An ci gaba da harbe-harben na kimanin minti 20 kuma sai da muka kwanta a kan kirjinmu muka riƙa gangarawa muka nisanta daga wajen saboda tsananin hatsarin da zai iya faruwa. Edita na sai ya tunkari daya daga cikin sojojin don ya bayyana mu a matsayin 'yan jarida kafin su ba ƙyalemu mu wuce lami lafiya'' in ji Damilola.
Wanene ya kashe kyamarar naɗar bayanai ta CCTV?
Wani kace-nacen da ya dabaibaye harbe-harben na Lekki shi ne rashin kyamarorin sa ido a daren da abin ya faru.
Da yake jawabi a wurin zaman kwamitin bincike, Manajan Daraktan Kamfanin Lekki Concession wanda ke kula da Lekki toll gate , Abayomi Omomuwasan, ya ce matsalolin hanyoyin sadarwa sun sa kyamarar ta daina aiki da karfe 20:00, wato takwas na dare.
Da yake martani game da zargin da ake yi wa kamfanin cewa da gangan ya kashe fitilu a filin zanga-zangar, Mista Omomuwasan ya bayyana cewa saboda dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya, LCC ta janye ma'aikatan ta kuma hakan ya hana su sauya janareto a lokacin da wutar ta ɗauke.
Mutane nawa ne suka mutu?
Da yake maida martani game da zargin da ake yi cewa sojoji sun harbe mutane da yawa a wajen, Gwamna Sanwo-Olu ya shaida wa CNN cewa yanzu haka gawarwakin da aka haƙiƙance sune na waɗanda aka kashe na nan adane a mutuware, kuma mutum biyu ne, sannan ya yi kira ga waɗanda ke da shaidar da zata nuna an kashe wani nasu su gabatar da bayanai.
Sai dai, rundunar sojin Najeriyar ta musanta kashe wani a wajen. Birgediya Janar Taiwo ya faɗawa kwamitin cewa mutum ɗaya ne ya mutu sakamakon mummunan rauni a hanyar Admiralty yayin da 'yan sanda suka kawo wani mamaci daga yankin Yaba dake jihar ta Legas.
Har zuwa yaushe kwamitin zai ci gaba da zama?
Kwamitin yana karkashin jagorancin wani alkalin da ya yi ritaya, Doris Okuwobi, kuma ya hada da mambobi daga kungiyoyin farar hula, Hukumar Kare Hakkin Dan Adam, Cibiyar Sasanci ta Jama'a da wakilan matasa biyu.
Kwamitin shari'ar na jihar Legas ya karɓi koke-koke sama da 110 kuma ana sa ran zai saurari dukkan masu korafin tare da lauyoyinsu da shaidu da ke halarta.
Kwamitin mai mutane takwas wanda ya fara zama a ranar 27 ga Oktoba zai zauna na tsawon watanni shida don bincikar da'awar cin zarafin 'yan sanda da nufin gurfanar da jami'an da suka yi kuskure a gaban shari'a tare da bayar da shawarar a biya diyya ga wadanda abin ya shafa.