Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yakubu Gowon: Tsohon shugaban Najeriya ya ce ya bauta wa ƙasar bisa tsoron Allah
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) ya ce dan majalisar dokokin Birtaniyar nan Tom Tugendhat da ya zarge shi da sace rabin kudin da ke babban bankin Najeriya lokacin yana kan mulki shirme kawai yake yi.
Janar Gowon ya shaida wa BBC News Pidgin cewa ya bauta wa Najeriya bisa gaskiya da tsoron Allah, yana mai cewa ayyukan da ya yi ba boyayyu ba ne don haka kowa yana iya zuwa ya gan su.
Da yake martani ga zargin da Mr Tugendhat cewa ya sace rabin kudin da ke CBN a 1975 lokacin da aka yi masa juyin mulki, Janar Gowon ya ce dan majalisar "shirme kawai" yake yi.
"Abin da dan majalisar ya fada shirme ne kawai kuma ban san a inda ya samu wannan bayani ba. Na bauta wa Najeriya bakin kokarina a wadannan shekaru kuma nasarorin da na cimma a bayyane suke ga kowa."
Tsohon shugaban mulkin na Najeriya ya ce ba zai yi ja-in-ja kan batun ba domin kuwa mutanen da suka san shi sarai za su yi magana a madadinsa.
"Ba na son yin magana kan wannan batu domin kuwa wadanda suka san ni sosai sun ce abin da dan majalisar ya fada ba gaskiya ba ne."
A ranar Talata ne 'yan majalisar dokokin Birtaniya suka kada kuri'ar amince wa kasar ta sanya takunkumi kan wasu jami'an gwamnatin Najeriya wadanda suke da hannu wajen cin zarafin masu zanga-zangar EndSARS.
A yayin da suke muhawara ne Mr Tugendhat ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa ne suke kawo tarnaki wajen ci gaban Najeriya, yana mai bayar da misalin cewa Janar Gowon ya sace rabin kudin da ke babban bankin kasar ya kai su London lokacin da ya sauka daga mulki.
Janar Gowon ya mulki Najeriya tsakanin 1966 zuwa 1975 kafin a kifar da gwamnatinsa yayin da yake halartar taron kungiyar Hada Kan Afirka da ake gudanarwa a Kampala, babban birnin Uganda.
Daga can ne kuma ya tafi Ingila, inda ya zama dalibi a Jami'ar Warwick University.