Rikicin APC: Fashola ya ce dole a mutunta tsarin karɓa-ƙarba kujerar shugaban ƙasa a APC a 2023

Ministan Ayyuka da Gidaje na Najeriya kuma tsohon gwamnan Legas Babatunde Raji Fashola ya ce ya zama wajibi a girmama tsarin karɓa-karɓa na jam'iyya mai mulki ta APC gabanin zaɓukan shekarar 2023.

Fashola ya bayyana hakan ne a yayin da yake wata ganawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, inda ya roƙi shugabannin jam'iyyar da su girmama yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓar da aka cimma a shekarar 2015.

A tare da ministan a yayin ganawar akwai wasu manyan ƴan APC da suka haɗa da tsohon shugaban jam'iyyar APC na kudu maso kudancin ƙasar Hilliard Eta da kuma Darakta Janar na gidan rediyon Najeriya Voice of Nigeria, Osita Okechukwu waɗanda suka goyi bayan ministan.

Wannan magana ta ministan na zuwa ne bayan da a ranar Litinin Darakta-Janar na Ƙungiyar Gwamnonin APC, Dr. Salihu Lukman, ya dage cewa za a bai wa dukkan mambobin jam'iyya damar shiga takara a 2023.

A hirarsa da ƴan jarida, Lukman ya yi watsi da "jita-jitar" da ake yaɗawa cewa jam'iyyar APCn ta cimma yarjejeniyar tsarin karɓa-karɓa.

Ana ganin Mista Fashola ya yi batunsa ne a matsayin mayar da martani kan zancen Mista Lukman, da zargin son rusa tsarin da aka shimfiɗa na sake miƙa mulki ga arewacin ƙasar bayan saukar Shugaba Muhammadu Buhari.

"Maganar gaskiya a nan ita ce abin da yake sa yarjejeniya ta zama muhimmiya shi ne girmama yadda aka cimmata wala a rubuce ko da baka. Idan an rubuta ta, to babu batun yin shari'a a kanta tun da an ruga an rubuta ne kuma an sanya hannu.

"Amma yarjejeniyar da kuka cimma da baki a tsakaninku a matsayin ƴan uwa bai kamata a ƙi mutunta ta ba, dole ne a girmama ta," in ji Mista Fashola.

Ya ƙara da cewa: 'Dukkan jam'iyyun siyasa tamkar gidajen rawa ne ta yadda za mu iya amincewa mafi ƙarancin shekaru shi zai yi jagoranci ko kuma wanda ya fi yawan shekaru ne zai zama shugaba, ko kuma mace ko namiji, wannan shi ne abin da mutane suka fi bai wa muhimmanci."

Manema labarai sun tambayi Fashola ko yana da aniyar tsayawa takara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a 2023, inda ya ce ''Ni ɗan jam'iyyar APC ne kuma ina son shugabanci nagari saboda a ganina babban abu a siyasa shi ne shugabanci nagari.

A shekarar 2013 ne aka samar da jam'iyyar APC bayan da jam'iyyun CPC da ACN da ANPP da APGA da sabuwar PDP suka haɗe waje guda.

Tun bayan zaɓen shekarar 2015 jam'iyyar APC ta fara samun kanta cikin rikice-rikicen cikin gida da suka ƙi suka ƙi cinyewa. Hana tasa wasu masu sharhi a Najeriyar ke ganin za a iya samun gagrumin rabuwar kai gabanin zaɓen 2023.