Rikicin APC: 'Kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu'

Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraren hira da Gwamna Mai Mala Buni:

Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC mai mulki ta Najeriya, Maimala Buni, ya ce kwalliya ta soma biyan kudin sabulu a yunkurin da yake na sulhunta rikicin jam'iyyar.

Cikin hirar da BBC ta yi da shi, Mai Mala Buni ya ce lokaci bai kure musu ba a yunkurinsu na shawo kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar.

"Muna da isasshen lokaci, dole ne jam'iyya babba kamar APC ta samu irin nata rigingimun ba tare da an bari lokaci ya ƙure ba shi ne babban abin farin ciki a gare mu."

Rikicin ya yi sanadin raba kan ƴaƴan jam'iyyar manya da kanana, har ta kai ga wasu daga ciki na sauya-sheƙa.

A watan jiya ne aka nada Gwamna Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC bayan shawarwarin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar.

An dora masa ɗawainiyar sasanta 'ƴa'ƴanta da kuma shirya ƙwarya-ƙwaryar babban taron jam'iyyar don zaben sabbin shugabanni nan da watanni shida masu zuwa.