'ASUU da gwamnatin Najeriya sun saka rayuwarmu cikin mummunan hali'- Daliban jami'o'i

An sha zama a na tashi baram-baram tsakanin gwamnati da ASUU

Asalin hoton, @FOTONUGGET

Bayanan hoto, An sha zama a na tashi baram-baram tsakanin gwamnati da ASUU

Bayan shafe lokaci mai tsawo a na yajin aiki sanadiyyar ja-in-ja tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya, daliban jami'o'in na ci gaba da kokawa kan halin da rashin jituwar ya jefa su.

Ɗaliban jami'o'in ƙasar na ci gaba da bayyana damuwa game da kiran da ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta yi wa mambobinta cewa su nemi wata hanyar dogaro da kai.

Bugu da kari kuma ASUU ta sanar da iyaye da su kansu ɗaliban jami'o'in da kada su sa ran komawarsu makaranta a nan kusa.

Matakin dai ya biyo bayan zargin da ƙungiyar ASUU ta yi wa gwamnati, na nuna halin ko-in-kula wajen biyan buƙatunsu, da kuma dakatar da biyansu albashi tsawon wata takwas.

ASUU ta ce ta fahimci cewa matsalar da a ke ciki ta kasancewar makarantu a rufe da kuma zaman dalibai a gida ko a jikinta.

A kan haka ta daukin matakin sanar da daliban jami'o'i cewa su cire rai da komawa makaranta yanzu.

Sai dai wannan labari bai zo wa daliban da dadi ba ko kadan, kuma kamar yadda wasunsu suka shaida wa BBC, kungiyar malaman jami'o'in da kuma gwamnatin Tarayya sun jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali kan kasa warware matsalar da ke tsakaninsu.

A cewar wata daliba: "Wallahi ba ku kyauta mana ba,ai sai ku ji tausayinmu mu 'ya'yan talakawa. Wata takwas muna zaune gida ba aikin fari balle na baki ai dole mu tashi mu nemi sana'ar hannu."

An sha zama a na tashi baram-baram tsakanin bangaroran biyu a dalilin kin amincewa da bukatun juna.