Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama 'yan sandan da suka kashe wasu matasa a Kano
Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wasu jami'anta da ake zargi da kisan wasu matasa a karshen mako.
Wasu iyayen matasa sun shiga ɗimauta da rokon a bi kadin rayukan ƴaƴansu da ake zargin ƴan sanda da hallaka su.
Lamarin ya janyo tunzuri inda matasa suka yi kone-konen tayoyi a unguwar Sharaɗa da ke cikin birnin Kano.
Wannan yanayi da iyayen matasan suka tsinci kan su na zuwa ne makonni da gudanar da gagarumar zanga-zanga kan cin zalin da ƴan sanda ke aikatawa a fadin ƙasar, lamarin da daga karshe ya juye zuwa tarzoma.
Mene ne laifin matasan?
Ana ci gaba da zaman makoki da juyayin mutuwar Ibrahim Sulaiman, mai shekara ashirin da takwas da aka daɓa wa wuka da kuma Abubakar Isah ɗan shekara talatin da biyu da aka harbe.
Ana zargin ƴan sandan sashen Anti-daba mai ƙaurin suna a Kano da waɗannan kashe-kashe a layin ƴar kuka cikin unguwar Sharadan Malam ta ƙaramar Hukumar Birni.
Wani shaida ya ce suna zaune a wurin wani mai shayi ne cikin daren Asabar sai ga ƴan sandan uku, biyu cikin kayan sarki, ɗaya kuma a farin kaya.
A cewarsa da zuwansu sai suka yi yunƙurin kama wani yaro a wurin, amma ya tsere kuma nan take suka bi shi.
Ganau ɗin ya ce ganin haka sai ɗan'uwan yaron ya bi su don ya ga abin da ke faruwa.
Ƴan sandan dai sun kama ɗan uwan tare da ƙanin, lamarin da ya sa mutanen wurin suka buƙaci sanin dalili, a nan ne fa gardama ta ɓarke.
"Wanda aka harba muna tare da shi, ɗan sanda ya yi barazanar harbe shi ai kuwa sai ya bude masa wuta, sannan ɗayan kuma wuka suka caka masa.
Mun je asibiti har an sa masa ruwa amma cikin dare Allah ya karbi ransa."
Me iyayensu ke cewa?
Mahaifin marigayi Abubakar, Malam Isah Ibrahim ya shaida wa BBC cewa shi ne babban ɗansa kuma yana da aure har da ƴaƴa biyu.
Ya kuma zargi cewa rashin iya aikin ƴan sanda ne ya kai ga mutuwar ɗansa.
"Na yi masa aure da ƴaƴansa, aikin carpenter ya ke yi, ni dai abin da nake so shi ne gwamnati ta bi kadin rayukan ƴaƴan mu"inji mahaifin Abubakar.
Malama Hauwa'u Abdulwahab, mahaifiya ga Ibrahim Sulaiman wanda aka daɓa wa wuƙa, ta ce ta ji mugun jin da ba ta taɓa jin irinsa ba a rayuwarta ranar da abin ya faru.
"Ta ce an cuce ta an kuma zalun ce ta, domin ɗanta na da imani baya faɗa, kowa nasa ne, shi ke daukan nauyi da dawainiyar iyayensa kasancewa mahaifinsa ya tsufa ba shi da karfi.
"Shi ne yarona na biyu, shi yake tausaya mana, baya sata baya shan komai amma aka rabani da shi", in ji mahaifiyar Ibrahim.
Malama Hauwa'u cikin hawaye ta roki a bi mata hakkinsu a hukunta masu hannu a mutuwar ɗanta.
Me ƴan sanda ke cewa?
DSP Haruna Abdullahi shi ne kakakin rundunar 'yan sandan Kano kuma ya shaida wa BBC cewa an kaddamar da bincike bisa umarnin kwamishinan yan sanda.
An tattaro jami'an da suka fita aiki a wannan dare an kai su Bombai hedikwatar ƴan sanda domin bincikar su.
DSP Haruna ya kuma ce duk wanda ke da bayani za a tuntube shi. Sannan aikin ƴan sanda ne tabbatar da cewa an gurfanar da mai laifi a Kotu.
Sharhi
Zargin kisan azarɓaɓi, da cin zarafi da kuma wuce gona da irin da ake yi wa ƴan sanda a Najeriya, abu ne da ya zama ruwan dare, na baya-bayan ya kai ga gagarumar zanga-zangar da ta yi matuƙar ta da hankalin ƙasar.
Sai da hukumomi sun rushe sashen yaƙi da 'yan fashi ko SARS tare da maye gurbinsa da wata sabuwar runduna, a yunƙurinsu na kawo ƙarshen cin zalin 'yan sanda.
Amma da alama abin da ke faruwa yanzu a Kano, na nuna akwai jan aiki gaba.
Karin labaran da zaku so karantawa