Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'yan bindiga ke sanya wa manoma haraji kafin girbi a Zamfara
Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren rahoton Abdussalam Ibrahim Ahmed:
"['Yan bindigar] sun aza mana kudi misalin N800,000 domin mu ba su mu yi aikin amfanin gonarmu kuma mun biya."
Wadannan su ne kalaman wani mutum da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa suka sanya wa haraji kafin su amince ya yi girbin amfanin gonarsa a ƙauyen Ɗan Kurmi da ke ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara a Najeriya.
Irin wadannan kalamai ne suke fitowa daga bakunan galibin jama'ar jihar ta Zamfara, wadda ta dade tana fama da hare-haren 'yan bindiga da ke kashe mutane, su sace wasu kana su yi wa mata fyade.
Mutumin ya shaida wa BBC cewa: "Akwai kauyuka makwabtanmu irin su Duhuwar Saulawa, Duhuwar Maikulungu, Bauɗi, Zagadi, Doka da Tungar Makeri; wadannan kauyukan babu inda ba su aza wa mutane kuɗi ba kuma sun biya. Bayan sun biya kudin kuma idan suka je aikin [gona] sai 'yan bindiga su ɗauke su."
Wani mutum da ke zaune a wani kauyen ya shaida mana cewa: "Yanzu abu mafi tashin hankali shi ne maharan nan sun dawo da wani sabon salo...kamar abin da ya faru a kauyen Duhuwar Maikulungu inda wani manomi ya buga waken suya buhu goma. Bayan sun gama aiki an ɗinke sai 'yan bindigar nan suka kori manoman suka yi awon gaba da waɗannan kayan noman da suka cira."
A cewar waɗannan manoma, 'yan bindigar sun raba su da kayan amfanin gona na miliyoyin naira sannan ba su cika alkawarin da suka ɗauka na kin sace su ba.
Hakan ya sa suna kwana kullum ido ɗaya a buɗe sannan sun talauce domin kuwa an kwace kayan amfanin gonarsu da kuma 'yan kuɗaɗen da ke hannayensu.
"Ka ga irin su Duhuwa Saulawa sun biya kudin fiye da naira dubu ɗari uku amma duk da haka dajin ya kasa shiguwa. Yanzu wake idan ka shiga gonakinmu ga shi nan fari tas a kasa, shinkafa kuma ta ƙanbule tana son yanka amma babu dama," in ji shi.
Sun yi kira ga hukumomi sun kai ƙara jami'an tsaro domin ba su kariya.
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara ta bakin kakakinta SP Mohammaed Shehu ta yi kira ga mazauna ƙauyukan su daina bayar da haraji ga 'yan bindigar tana mai cewa yin hakan zai ƙarfafa gwiwar su su ci gaba da kai musu hare-hare.
"Kullum muna ƙoƙari muna wayar da kan jama'a cewa su guji bayar da kudin domin yin hakan ne yake ƙara wa su wadannan 'yan bindiga ƙarfin gwiwa na zuwa suna sa irin wadannan kudaden," a cewar SP Shehu.
Sai dai mutanen ƙayukan sun ce babu yadda za su yi su daina biyan haraji ga 'yan bindigar ganin cewa gwamnati ta kasa kare rayukansu da dukiyoyinsu.
A baya, gwamnatin jihar ta Zamfara ta yi sulhu da 'yan bindigar domin su daina kai hare-hare amma batun na ci gaba da yin ƙamari.