Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Har ɗaki aka shigo aka caccaka min wuƙa domin a ƙwaci wayata a Kano'
Rukayya Sulaiman, wata matashiya ce a birnin Kano, wadda ta tsinci kanta a halin firgici da ɗimuwa lokacin da wani matashi ya kutsa gidansu ya ƙwace wayarta bayan da ya daɓa mata wuƙa a sassan jikinta.
"Misalin ƙarfe uku dare ina kwance a cikin gidan sauro. Na juya haka kawai sai na gan shi a dab da bakin gadona yana zaune. Da farko sai ya mare ni sai ya rarumo ni ya matse min bakina, na yi ihu amma babu wanda ya ji ni.
Har ya tafi sai ya dawo ya ɗaga rigarsa ya ɗauko wuƙa sai ya karɓe wayata ni ma Allah ya ba ni sa'a na fizge ta. Har ya tafi sai ya dawo sai ya zaro wuƙa sai ya rinƙa caccaka min wuƙar a bayana da wuyana. Ya caka min wuƙar wuri bakwai."
Ruƙayya dai ɗaya ce daga cikin ɗaruruwan mutanen da suka fuskanci irin wannan aika-aika ta masu ƙwacen waya a birnin na Kano.
Matsalar ƙwacen waya a Kano babu wanda ta bari, inda mutum na tsaka da tafiya a kan hanya sai dai ya ji A dai-daita sahu ɗauke da matsa wani lokacin uku ko huɗu sun sha gaban abin hawanka tare da zare makami su nemi ka ba su wayarka idan mutum ya ki kuwa su buga masa makami.
Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sha faɗin cewa tana maganin wannan matsala inda ta ce ta kama gomman irin waɗannan matasa kuma tana shirin gurfanar da su gaban ƙuliya.
Ko a makon da ya gabata sai da rudunar ta ce ta yi holin masu aikata irin wannan ɗabi'a da ta ce ta kama su a lokacin da ake bikin Takutaha a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, bayan samun bayanan sirri na cewar matasan sun shirya ƙwacen wayoyi inda aka kama su da makamai.
Kwamishin 'yan sandan rundunar ta Kano, Habu A Sani, ya ce sun fito da sabbin dabaru wajen magance wannan matsala sannan an sami raguwar matsalar a cikin jihar.
"Daga cikin laifukan da muka gano akwai dawowar daba inda matasa masu ƙarancin shekaru daga 15 zuwa 30 su ne suka fi yawa.
''Amma an samu raguwar masu aikata laifin. Sai dai a lokacin bikin Takutaha ne muka samu masu laifin da yawa."
Kwamishina Habu ya kara da cewa "Mun kama mutum fiye da 3000 da laifin ayyukan daba. Sannan mun samu wayoyi fiye da 400 da aka ƙwace kuma mun mayar wa da masu su."
To sai dai duk da ikirarin da rudunar ƴan sandan ke yi na cewar an sami raguwar wannan matsala, har yanzu al'amarin na da ban tsoro inda yanzu haka a birnin Kano mutane da dama na shakkar fito da waya domin amsa kira a fili.
Hakan dai na faruwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin jihar ta Kano ke cewa tana kafa na'urorin naɗar faifan bidiyo a wuraren da ake samun yawan hada-hadar al'umma a birnin Kano.