Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sufeton 'yan sandan Najeriya ya ce a ɗauki mataki kan lamarin Rahama Sadau
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bai wa kwamishinan 'yan sandan Jihar Kaduna umarnin ɗaukar mataki kan fitacciyar 'yar fim ɗin nan Rahama Sadau, bayan wani ya kai ƙararta ga 'yan sandan kan wasu hotuna da ta wallafa da suka jawo ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Sai dai a bayanan da BBC ta samu, 'yan sandan ba su kai ga kama ta ba saɓannin yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito, sai dai wata majiya mai ƙarfi ta nuna cewa tana ƙoƙarin haɗa tawagar lauyoyinta da za ta je da su ofishin 'yan sandan domin kai kanta.
Cikin wata wasiƙa da Babban Jami'in Ofishin Sufeto Janar DCP Idowu Owohunwa ya rattaɓa wa hannu, Mohammed Adamu ya umarci wamishinan 'yan sanda na Jihar Kaduna ya gaggauta ɗaukar mataki don tabbatar da cewa wannan lamari bai haifar da wani abu na rashin tsaro da tayar da hankalin jama'a ba.
Koken da aka kai wa 'yan sanda kan Rahama Sadau
A takardar koken da Alhaji Lawal ya aika wa babban sufeton, ya shaida wa babban sufeton cewa abin da Rahama ta aikata zai iya jawo rikici domin kuwa tuni wasu malamai da matasa suka fara barazanar ɗaukar mataki, a cewarsa.
Ya kuma yi wa babban sufeton matashiya kan abin da ya faru a Kano a 'yan kwanakin nan da kuma a Faransa wanda ya ce dama tuni al'ummar Musulmi abin ya kai su bango.
Ya kuma buƙaci babban sufeton ya yi la'akari da cewa bai kamata Najeriya ta ƙara tsunduma cikin wani rikici ba a daidai lokacin da take ƙoƙarin farfaɗowa daga tarzomar da ENDSARS ta jawo.
Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Alhaji Lawal Gusau, wanda ya kai Rahama ƙara domin jin ƙarin bayani, amma bai ɗaga waya baya.
Sai dai Mujallar Fim ta ruwaito cewa Alhaji Lawal Gusau ɗin sananne ne wajen shiga al'amuran da suka shafi harkar fina- finan Hausa, domin kuwa, ko a kwanakin baya sai da ya kai ƙara a kan bidiyon tsiraici wanda ake zargi na Maryam Booth ne da aka yi ta yaɗa shi a kafafen sada zumunta a kwanakin baya.
A cikin makon nan ne dai Rahama Sadau ɗin ta wallafa wasu hotuna waɗanda suka nuna surar jikinta, wanda hakan ya jawo wani ya yi maganar ɓatanci game da Manzon Allah (SAW) a ƙasan hotunanta da ta saka.
Sai dai daga baya jarumar ta fito ta ce sam ba da yawunta aka yi waɗannan kalaman ɓatancin ba, inda har ta yi bidiyo tana kuka tana roƙon gafarar Musulmai da waɗanda abin ya ɓata wa rai.
Tun kafin ta nemi gafarar, abokan sana'arta da dama na Kannywood sun fito sun yi mata raddi mai zafi, haka ma wasu sanannun mutane a kafafen sada zumuntar sun yi mata raddi da jan kunnenta.
Sai dai bayan haƙurin da ta bayar da kuma nadamar da ta yi, wasu sun sassauta kalamansu kanta da ba ta shawarar kada hakan ya sake faruwa, wasu kuma na nan a kan bakarsu na cewa ba za su yafe mata ba.