"Mun gaji da wulaƙanta addininmu": Dalilin ƙauracewa sayen kayan Faransa

    • Marubuci, Daga Sodaba Haidare
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Zanga-zanga ta yi ƙamari a ƙasashen musulmi daga Turkiyya da Bangladesh da Jordan to Malaysia, tare da yin kira ga jama'a su ƙauracewa kayan da ake samarwa a kasar Faransa.

Shaguna da dama sun cire dukkanin kayan da aka rubuta sunan Faransa a jikinsu, sannan maudu'in neman a kauracewa kayan ya samu karɓuwa sosai a shafukan sada zumunta, akalla mutane dubu dari ne suka yi tsokaci a kai a mako guda.

Martanin na zuwa ne, bayan kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron, sakamakon kisan malamin makarantar nan da ya nuna zanen Annabi Muhammad (S A W) ga ɗalibansa yayin da yake basu darasi dangane da 'yancin albarkacin baki.

Shugaba Macron ya ce ''An kashe malamin ne, saboda masu kaifin kishin islama na son karbe ragamar alkiblarmu'', amma Faransa ''ba zata janye zanen barkwancin ba.''

Zanen da ake magana na nuna wani mutumi da aka bayyana a matsayin Annabi Muhammad, kuma an wallafa shi ne a jaridar barkwanci ta Charlie Hebdo tun shekarar 2006, lamarin da ya ɓata ran musulmin duniya saboda yadda suke ganin cewa hakan batanci ne ga Annabi.

Shugaban na Faransa ya samu yabo da jinjina a wajen 'yan ƙasar da dama sakamakon kare Faransa, a matsayinta na 'yar ba ruwana da kowane addini.

Sai dai a kasashen musulmai lamarin ba haka yake ba, domin kyara da tsanar shugaban ce ta samu wajen zama, baya ga dubban mutanen da suka kwarara a kan tituna suna Allah-wadai da kamalansa.

Mishi Khan - Tauraruwa ce da ke zaune a Islamabad a Pakistan

Na kasance mai amfani da kayan kwalliyar da ake samarwa a Faransa, musamman man gashi na L'Oréal wanda ake samun shi cikin sauki a nan Pakistan. Amma a yanzu ina karanta rubutun da ke jikin komai da na siya, domin in tabbatar da cewa ban saki kayan da aka samar a Faransa ba.

A yanzu, na maye gurbin kayan Faransa da nake saya da na nan gida Pakistan.

Kun san dalili ? - saboda bai kamata ace shugaban wata kasa ya wayi gari kawai ya hau cin mutuncin wani addini da masu bin sa ba.

Yanzu haka ina ta kiran mutane a shafukan sada zumunta su kauracewa kayan Faransa. dalilina a bayyana yake, ina yin hakan ne domin in kare addinin musulunci.

Mun gashi da irin yadda wasu mutane ke bara addinin da muke bi da kuma wani ya fi mana kowa wato Annabi Muhammad, muna ta yafe wa wadanda ke yin haka, to yanzu an kai mu bango!.

Ina ganin Macron na yin abin da yake yi ne da gan-gan domin kuntatawa al'ummar musulmai, kamar ka yakushi mutun ne sannan kace masa ''Ji mana, da zafi?'.

Ya yi kuskure, sannan kalamansa na iya janyo kyamar musulmai, wanne shugaban kasa ne zai gwara kan 'yan kasarsa in ba shi ba ?.ai kamata ya yi ace ya hada kan jama'a.

Lokacin da na fara ganin zanen Charlie Hebdo, na ji takaici, rasa me zance na yi, na kauracewa ganin hoton tsawon lokaci, amma lokacin da na gani gaskiya raina ya baci, na yi kuka sosai.

Latife Ozdemir - Daliba ce a birnin Santambul dake Turkiyya

Kayan Lancôme, da Garnier da BIC dukkansu kaya ne da nake amfani da su kusan yau da kullum, amma bayan abin da ya faru, daga yanzu na daina siyansu.

Na dauki wannan mataki ne saboda in nuna wa duniya cewa daga yanzu mun daina yadda da irin wannan.

Yana da muhimmanci ga mu musulmai mu yi Allah wadai da wannan abu, ya kama a ji mu, domin an dade ana toshe mana baki.

Mujallar Charlie Hebdo ta sake wallafa wani hoton ɓatanci da ke nuna shugaban mu Recep Tayyin Erdogan, yana sanye da karamar riga ba wando yayin da ya daga kwalbar barasa, sannan ya ɗaga wandon wata mata musulma sanye da hijabi.

A matsayi na na macen da ke sanya hijabi na ji takaici matuka dangane da abin da na gani.

Mata musulmai iri na na kokari ba dare ba rana domin kare martabar addinin musulunci da kuma samun damar damawa da mu a al'amura, wannan na iya kawo mana koma baya.

Wannan zane da na gani na nuna mana cewa mata ba komai ba ne, sannan kasashen yamma ba za su taba kallonmu a matsayin dai-dai da wadanda ba musulmai ba.

Kamata ya yi ace zanen barkwanci na haifar da tunani mai zurfi, amma a maimakon haka suna amfani da wannan hanya wajen cin zarafin musulunci da musulmai.

Zane irin wannan, na kara rura wutar al'amura ne kawai, bana jin haka muke fatan duniyar ta kasance, ace wannan na kyarar wannan ko wannan na cin zarafin wannan.

Hiba Mohamed Moussa -Daliba a Mauritania

Na shiga zanga-zangar da aka yi a Nouakchott tare da dukkanin 'yan gidanmu, da sauran abokai, domin yin Allah wadai da abin da ke faruwa a Faransa.

Mun kauracewa dukkanin kayan Faransa, bisa fatan tattalin arzikin kasar zai rushe, sannan Macron ya nemi afuwar al'ummar musulmai biliyan biyu da ya batawa rai da munanan kalamansa.

A baya ina amfani da turarukan da ake samarwa a Faransa, kamar Lacoste amma da zarar wanda nake da shi ya kare, bazan sake siya ba kuma.

Na rubutawa shugaba Emmanuel Macron wasiƙa, ina neman ya nemi afuwarmu. a cikin wasikar na tambaye shi ko malamin da aka kashe ya cancanci a girmama shi? to shi kuma Annabinmu fa? Wadanda shi ma malami ne.

Abin da ya fi tsaya mana a wuya shi ne kalamansa na kyamar musulunci, tare da bayyana addininmu a matsayin wanda ke goyon bayan a kashe, wannan rashin adalci ne, da kuma kokarin angiza mu, ba zamu lamunci hakan ba.

Zancen gaskiya shi ne ace shugaban wata ƙasa kamar Faransa ya dauki wasu hotuna da ke zaman ɓatanci ga wani bangare guda sannan ya goyi bayan abin da aka yi ba 'yancin fadin albarkacin baki ba ne.

Na yi ƙankanta in iya tuna lokacin da mujallar Charlie Hebdo ta tizanen barkwancin Annabi, amma ina iya tuna lokacin da aka kai wa ofishinta hari, har kowa ya rika canja hotonsa na shafukan sada zumunta zuwa tutar Faransa domin taya su jimami.

Tun daga nan nan na rika kokarin kaucewa ganin irin wadannan hotunan, amma ranar nan ina cikin duba Twitter, kwatsam sai ga hoton na gani, na ji takaici, me ya sa ba za a mutunta addinin musulunci kamar yahudawa ba da kiristanci?