EndSars: Hotunan yadda aka gudanar da zanga-zangar a Najeriya
An kwashe fiye da mako biyu ana zanga-zanga kan cin zarafin da rundunar 'yan sandan SARS, wadda aka rusa, ta rika yi wa 'yan Najeriya.

Asalin hoton, Reuters


Asalin hoton, EPA
Lamarin ya soma ne sakamakon zargin da 'yan Najeriya ke yi wa rundunar SARS wajen daure mutane ba bisa ka'ida ba, da cin zalinsu da kuma kashe su, abin da ya kai ga rusa ta.
Shugaba Buhari ya rusa rundunar ranar 11 Oktoba.


Asalin hoton, EPA
Tun daga lokacin, masu zanga-zangar sun yi ta kira kan kawo sauyi ga tsarin tsaron kasar da kuma yadda suke ganin za a kawo sauyi ga kasar baki daya.


Asalin hoton, Reuters


Asalin hoton, EPA


Asalin hoton, Getty Images
An zargi jami'an tsaron najeirya da kashe masu zanga-zanga da dama musamman a Lagos, babban birnin kasuwancin Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Ganau sun ce an kashe akalla mutum 12 sannan aka jikkata mutane da dama lokacin da sojoji suka bude wuta kan masu zanga-zanga.
Kungiyar Amnesty International ta ce ta "samu bayanai masu kwari" kan kashe-kashen da aka yi.
Gwamnan jihar ya ce babu wanda ya mutu, ko da yake mutum 25 aka jikkata.
A London, masu zanga-zangar sun kwashe kwanaki suna fitowa kan tituna.

Asalin hoton, Getty Images


Asalin hoton, Getty Images


Asalin hoton, Joseph Okpako
An gudanar da zanga-zanga a wajen ofisoshin jakdancin Najeriya da ke kasashe da dama, ciki har da Nairobi, Kenya (a hoton da ke kasa)...

Asalin hoton, Getty Images
...da kuma ofishin jakadancin Najeriya da ke Pretoria, Afirka ta Kudu (hoton da ke kasa).

Asalin hoton, PHILL MAGAKOE


Asalin hoton, Getty Images
.











