EndSars: Ƴan sanda sun buɗe wa dubban masu zanga-zanga wuta a Lagos

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun mutu bayan sojoji sun buɗe wuta kan dubban masu zanga-zangar EndSars a dandalin Lekki toll gate da ke birnin Legas a kudancin Najeriya da yammacin Talata.
Ganau sun shaida wa manema labarai cewa an kashe akalla mutum 12 yayin da aka raunata da dama bayan soji sunbuɗe wuta kan masu zanga-zangar.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce ta samu kwararan bayanai kan kashe-kashen da suka faru.
Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa jami'anta sun kashe masu zanga-zangar. Hukumomi sun yi alkawarin gudanar da bincike.
Masu zanga-zangar sun ci gaba da yin ta ne bayan da gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa'a 24 a jihar a ranar Talata da safe sakamakon ƙona wani ofishin yan sanda da aka yi.
BBC tana cikin nuna bidiyon ci gaban zanga-zangar kai tsaye a shafinta na Facebook a lokacin da aka fara harbe-harbe da bindiga a wajen.
Dubban mutane ne suka sake taruwa a dandalin na Lekki toll gate suna ci gaba da zanga-zangar.
Amma nan da nan sai komai ya hargitse wajen ya cuɗe. Babu tabbas kan ko mutum nawa ne suka jikkata a lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 6.45 na yamma agogon Najeriya.
Sannan babu bayanai a hukumance kan alkaluman mutane da suka mutu ko jikkata. Sai dai wani ganau ya tabbatar wa BBC cewa ya ƙidaya gawawwaki 20 an kuma jikkata sama da 50.
Tuni dai zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici tsakanin masu yin ta da wasu da ake zargin ƴan daba ne a wasu manyan biranen ƙasar da suka haɗa da babban birnin tarayya Abuja.
Shi ma wakilin sashen BBC Pidgin ya ce ya ga mutum ɗaya da ya jikkata.
Rahotanni na nuna cewa ƴan sandan kwantar da tarzomar sun yi ƙawanya sun zagaye masu zanga-zangar da suka ƙi guduwa.
Kuma sauran waɗanda suka rage ba su gudu ɗin ba sun haƙiƙance cewa za su ci gaba da zanga-zangar EndSars ɗin.
A yanzu gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayar da umarnin cewa ka da a fara aiki da dokar hana fitar sai ƙarfe 9 na daren yau saboda mutanen da cunkoson ababen hawa ya rutsa da su su samu damar koma wa gida.
Sojojin sun fara harba harsasai sama ne da farko, su kuma masu zanga-zangar suka fara amfani da abin wasan wuta don mayar wa sojojin martani, a cewar wakilin BBC Pidgin da ke wajen.
Wasu masu zanga-zangar dai suna cewa mutane sun mutu wasu kuma sun jikkata bayan faruwar lamarin.
Amma har yanzu rundunar sojin Njeriya ba ta ce komai ba.

Dama tun da farko a ranar Talatar Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya ya umarci baza 'ƴan sandan kwantar da tarzoma a duk faɗin ƙasar.
Sanarwar Muhammad Adamu, na zuwa ne yayin da ake samun ƙaruwar tashin hankali a wasu jihohi sakamakon zanga-zangar nuna adawa da cin zalin da ake zargin jami'an 'yan sanda na yi.
Tuni a wasu jihohin ma aka sanya dokar hana fita ta sa'a 24 kamar Jos da Ekiti da Abia.












