Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
#SecureNorth: Aisha Buhari ta bi sahun masu fafutuka kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya
Mai ɗakin Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bi sahun masu kira a kawo ƙarshen rashin tsaron da ke addabar Arewacin Najeriya.
Matar shugaban kasar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twitter ranar Asabar tare da wakar mawakin Kannywood, Adam A. Zango inda yake kokawa kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin Najeriya.
Sakon nata na ɗauke da maudu'in #Achechijamaa, wanda ke nufin a ceci rayuwar jama'a. Wakar na ɗauke da hotunan Shugaba Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaron kasar da ke nuna su a fadar shugaban ƙasa suna ganawa.
Baitin wakar na cewa:
"Don Allah a duba,
Taimakonka [Shugaba Buhari] muke nema
Arewa na kukaye,
Ana zubar da jininmu
Ana kashe al'umarmu
Ana ƙona dukiyarmu...
Masu amshin suna kiran sunan Baba, wato Shugaba Buhari.
Mai dakin shugaban kasar ta wallafa saƙon ne a yayin da 'yan Najeriya, musamman daga kudancin ƙasar ke tsaka da zanga-zanga kan gallazawar da rundunar 'yan sandan ƙasar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS, wadda aka rusa, take yi musu.
Suna amfani da maudu'in #EndSars don jawo hankali kan wannan matsala da ma wasu matsalolin da ke addabarsu.
Kazalika takwarorinsu na arewacin kasar suna tasu zanga-zangar kan taɓarɓarewar tsaro a yankin inda suke amfani da mau'du'in #SecureNorth don bayyana halin da yankin ke ciki.
Ɗaruruwan mutane ne suka mutu yayin da dubbai suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar a shekarun baya bayan nan.
Hakan na faruwa ne a yayin da yankin ke ci gaba da fama da hare-haren mayaƙan Boko Haram waɗanda aka kwashe shekara da shekaru ana fuskanta.
Mai ɗakin shugaban ƙasar ta dade tana korafe-korafe kan gwamnatin mijinta.