Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Senegal: Tijjaniya ta ɗage taron Maulidi na bana
Ɗariƙar Tijjaniya mabiya Malik ta ƙasar Senegal ta sanar da cewa ta ɗage yin babban taron maulidin Manzon Allah SAW na shekara-shekara da take yi a ƙasar saboda gudun yaɗuwar cutar korona.
A maimakon taron na ranar, Tijjaniya ta buƙaci mabiyanta su yi murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah SAW a cikin sirri a gidajensu, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar.
Fiye da kashi 90 cikin 100 na 'yan ƙasar Senegal Musulmai ne, kuma mafi yawansu mabiya Ɗariƙar Tijjaniya ne, kana suna da tasiri a kan harkokin tattalin arziki da na siyasar ƙasar da ke da mutum miliyan 16.
Tijjaniya na daga cikin manyan ƙungiyoyin Musulmai na Senegeal, kuma su kan yi maulidi a garin Tivouane da ke gabashin birnin Dakar kuma yake da nisan kilomita 90 zuwa can.
Dubban ƴan Tijjaniya ne ke zuwa garin don yin taron da suke kira da ''Gamou'', tun daga shekarar 1920.
Wani mai magana da yawun ƙungiyar a ranar Talata ya ce shugaban Ɗariƙar Tijjaniar Serigne Babacar Sy Monsour yana umartar mutane su zauna a gida.
''Babu abin da zai faranta masa rai irin ya samu damar sake haɗuwa da ku, amma ba za a tilasta wa kowa kan abin da ba zai yiwu ba,'' yana mai alaƙanta cutar korona da masifa.
Hukumomin lafiya na Senegal sun ce mutum 15,307 ne suka kamu da cutar tun ɓullarta ƙasar a watan Maris, inda mutum 315.
A yayin da ƴan Tijjaniyya suka soke taron nasu na bana, su kuwa Maridai wata mazahabar ta Sufi, sun gudanar da nasu babban taron a wannan watan da suke kora Magal.
Taron kan samu halartar dubun-dubatar masu ziyara zuwa birnin Touba da ke yankin tsakiyar Senegal, abin da ya sa aka soke shi saboda gudun kar cutar korona ta yaɗu sosai.
Mai magana da aywun Tijjaniyar ya ce, ''Akwai hanya dubu ta yi wa Allah godiya.''
''Yi wa mara lafiya addu'a abu ne mai lada da mutum zai iya yi,'' a cewarsa.
''Ko kuma gaya wa likitoci da malaman jinyarmu kalamai masu daɗi na ƙarfafa gwiwa, waɗnda suke aiki tuƙuru cikin wata takwas ɗn d suka gabata ba gajiyawa.''