'Yadda fallasa cin hanci ya janyo na shiga halin ni 'ya su'

A jerin wasikunmu na 'yan jaridar Afirka, Hopewell Chin'ono na Zimbabwe ya yi bayanin yadda ya kwarba, sakamakon tsegunta wata badakalar cin hanci da rashawa a farkon wannan shekarar.

Na kasance cikin tsammanin abin da ka je ya zo, don haka lokacin da wasu mutane takwas dauke da manyan bindigu kirar AK47 suka iso kofar gida na sanye da fuskokin badda kama a safiyar ranar 20 ga watan Yuli, ban yi mamaki ba''

Na samu wani gargadi makonni bakwai da suka gabata, lokacin da kakakin jam'iyya mai mulki ya kira ni "marar gaskiya" kuma ya zarge ni da bata sunan dangin shugaban kasar.

Wannan ya faru ne bayan da na bankado wata badakala a kwangilar sayo kayayyakin yaki da cutar korona da aka bayar, abin da yasa aka kori ministan lafiyar da ya aikata wannan abu, kuma yanzu haka yake fuskantar tuhuma kan zargin.

Lokacin da jami'an suka nemi na fito daga gidana, na nemi ganin takardar sammacin da suka samu daga kotu, amma ba su nuna min ko daya ba.

Madadin haka suka bugi kofar gilashin dakin cin abinci na da bindiga, suka ratsa ta cikin dakina inda nake jiran su da waya ta, nake kuma haskawa duniya su kai tsaye.

Suka ja ni a kasa suka fita da ni ba tare da ko takalmi ba, harma suka nemi in bi ta kofar da suka fasa gilashinta don kawai in ji wa kaina ciwo.

Wannan shine farkon taskun da na shiga na kwanaki 45.

Ba ni kaɗai ba, an kama ni a wannan ranar tare da Jacob Ngarivhume, wani ɗan rajin siyasa wanda ya kira zanga zangar lumana ta nuna kyama ga cin hanci da rashawa.

An tuhume mu da laifin tayar da rikici, saboda na goyi bayan zanga zangar da ya kira duba da cewa kundin tsarin mulkin Zimbabwe ya bayar da damar jama'a su fito su nuna damuwarsu a duk lokacin da suke da bukatar yin hakan.

Sai dai wannan gwamnati mai ci ta shugaba Emmerson Mnangagwa na adawa da hakan.

Yayin da muke kurkukun Harare, mun sami ziyara daga babban jagoran adawa na Zimbabwe, Nelson Chamisa, wanda aka ce mana ya yi matukar batawa ofishin shugaban kasar rai.

Na yi zazzabi mai zafi a makon karshe na watan Agustan da ya gabata, asibitin gidan kurkukun ba su da ko da paracetamol don taimakawa marassa lafiya.

Lokacin da likitana ya zo kurkukun, asibitin ba shi da na'urar gwajin jini da zai yi amfani da ita, yawancin fursunonin sun koma gudanar da ibadunsu ne, yana da wuya ka samu wani na barci saboda hayaniya yayin ibada.

Wasu daga cikinsu suna can saboda laifukan da suka aikata, akwai kuma waɗanda suke ciki don ra'ayin siyasarsu, wasu an yanke musu hukunci duk da cewa ba su aikata laifin komai ba.

Na nuna rashin amincewa da tsarin da ake da shi a kurkukun, sakamakon haka ne ma muka sami karin manyan fitilu guda uku, da kuma takunkumi haka da aka raba mana saboda kariya daga korona.