Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hachalu Hundessa: An kama wadanda ake zargi da kisan sanannen mawakin Habasha
Hukumomi a Habasha sun kama mutun hudu da su ke zargi da kisan sanannen mawakinnan Hachalu Hundessa.
A na zargin mutanen da aikata laifukan ta'addanci kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.
Mutuwar Mr Hundessa ta haifar da zanga zanga, wadda daga baya ta rikide zuwa tarzomar da ta yi sanadin mutuwar mutun 150.
A lokacin an kama dubban jama'a, da su ka hada da sanannen dan siyasa Jawar Mohammed.
Haka ma Reuters ta ruwaito cewa a na tunanin wadanda a ke zargi da kisan Hachalu Hundessa sun hada baki da wasu mutane daban, a wani shirin aiwatar da kisan sanannun mutane a Habasha.
An harbe Hachalu a Addis Ababa a ranar 29 ga watan Yunin wannan shekara.
Ya kuma yi suna ne saboda wakokin 'yanci da neman hadin kan kabilar Oromo da ta fi kowace kabila yawan al'umma a Habasha.