Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Auren Fatima Ribadu da Aliyu Atiku: Mutane na tofa albarkacinsu kan auren ɗan Atiku da ƴar Nuhu Ribadu
Shekaru da dama da suka wuce, Nuhu Ribadu ne shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati EFCC, yayin da Atiku Abubakar yake matsayin mataimakin shugaban Najeriyar a lokacin.
A yau mutanen biyu na son zama surukan jina. Ga abin da muka sani zuwa yanzu kan lamarin.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa Fatima Ribadu, ƴa ga Nuhu Ribadu, tsohon shugaban EFCC, za ta auri ɗan tsohon mataimakin Najeriya Aliyu Atiku Abubakar.
Rahotanni sun ce za a yi auren ne ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2020, kamar yadda aka wallafa a katin bikin, wanda BBC ta gani.
Sai dai daga Fatima Ribadu har Aliyu Atiku, babu wanda ya ce komai kan lamarin har zuwa yanzu.
Aliyu Atiku Abubakar, shi ne Turakin Adamawa, inda ya gaji babansa Atiku ɗan takarar shugaban ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar PDP, bayan da ya zama Wazirin Adamawa a shekarar 2017.
Turakin Adamawa na ɗaya daga cikin muhimman muƙaman sarauta a Masarautar Yola.
Aliyu kuma ma'aikacin banki ne sannan daraktan kamfanin Priam Group, ɗaya daga cikin kamfanonin babansa. Yana kuma son ya gaji babansa ta fuskar siyasa.
Fatima Ribadu, ɗaya daga cikin ƴaƴan Nuhu Ribadu ce, tsohon shugaban hukumar EFCC.
Kuma babbar ƙawa ce ga ƴar Shugaba Muhammahu Buhari, Hanan.
A watan Disamban 2016, Hanan wacce ta ƙware a ɗaukar hoto, ta wallafa hotunan Fatima Ribadu a shafinta na Instagram.
Ƴan Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta kan auren manyan ƴan siyasar biyu daga jam'iyyu daban-daban masu adawa da juna.
Atiku Abubakar ɗan jam'iyyar PDP ne, yayin da Nuhu Ribadu yake ɗan APC.
Sai dai dukkan su ƴan asalin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ne.
Ga abin da mutane ke cewa kan auren
Alhaji IU Wakili @IU_Wakili ya ce: ''Ɗan Atiku (jigo a PDP) zai auri ƴar Nuhu Ribadu (jigo a APC), kai kuma ka daina yi wa maƙwabcinka magana kawai don ra'ayinku ya sha bamban a zaɓen 2019.
Ka tambayi kanka hakan ya dace?
I am МrMahumme @halexmahum ya ce: ''Dangantaka da yawa ta lalace a lokacin da Atiku da Ribadu suka fafata.
Gara ku san wannan, tabbas masu kuɗi ba sa faɗan da ba za a sasanta ba idan son ransu ya ratsa. A wajensu, hakan wasa ne kawai. A ƙarshe, za a bar mu mu ci kanmu ne kawai.''
larrymo231 @larrymo231 ya ce: Mutanen arewa sun fi kowa iya siyasa a Najeriya. A Kano na yi hidimar ƙasata kuma zan iya gaya muku cewa sun fahimci siyasa ba yaƙi ba ce.
''Suna iya samun bambancin ra'ayi a siyasance amma sam ba maƙiya ba ne. Ya kamata mu koya daga wajensu.''
Dami Agunloye @Dami4Change ya ce: ''Waɗannan matasan sun amince su zauna da juna tsawon rayuwarsu a matsayin mata da miji, kuma hakan ba shi da wata alaƙa da bambancin siyasar iyayensu.
''Wannan babban darasi ne da ya kamata a koya, kar ka zama mai hauka kan son APC ko PDP.''
Abdallah Yunus Abdallah @Abdool85 ya ce: Aliyu ɗan Atiku Abubakar na PDP zai auri Fatima ƴar Nuhu Ribadu na APC.
''Ku zauna ku ci gaba da faɗa da junanku.''