Sadiya Farouq: Da gaske ministar ta karkatar da N2.67bn da sunan ciyar da ɗalibai?

Lokacin karatu: Minti 5

An wayi garin Talata ana ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta musamman Twitter a Najeriya kan zargin da hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta yi cewa an karkatar da kudi har naira biliyan 2.67 da aka ware domin ciyar da 'yan makaranta a lokacin kullen korana.

A jiya Litinin ne shugaban hukumar ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye, a wani taro kan rashawa da aka gudanar a fadar shugaban kasa a Abuja ya bayyana cewa an karkatar da dimbin kudin, kuma sun gano su a asusun ajiyar bankin wasu ma'aikatan gwamnati.

Farfesa Bolaji ya ce an fahimci cewa an fito da tsarin asusun bai-daya na TSA ne domin sa ido kan fitar da kudi da kasafta su.

Amma duk da haka sai da aka karkatar da wani bangare na wannan kudi, don haka suna gudanar da bincike kan batun.

Sai dai fitar labarin ba da jimawa ba aka yi ta yayata shi a jaridun Najeriya da zargin ma'aikatar ayyukan jin-kai da Minista Sadiya Farouq ganin cewa ma'aikatar ce ta rinka kulla da harkokin taimako a lokacin kullen korona da rarraba agaji ga magidanta, makarantu a jihohin kasar da ma birnin tarayya Abuja.

Sa'o'i kadan da fitan labarain ma'aikatar jin-kai ta mayar da martani a wata sanarwa da ta fitar da ke musanta akwai hannu ta ko na minista Sadiya da ma'aikatan ta.

Amma daga bisani da yammacin ranar Talata sai hukumar ICPC ta yi ƙarin haske game da batun inda ta ce shugaban nata yana magana ne kan ciyar da ɗaliban da suke makarantun kwana a kwalejojin gwamnatin tarayya waɗanda suke gida a lokacin annobar korona.

A cewar hukumar wannan ba yana nufin shirin ciyar da ƴan makaranta da ma'aikatar jin ƙai take kula da shi.

Hukumar ta ce ta gano cewa an karkatar da wasu kuɗaɗe da aka ware domin ciyar da ƴan makarantar sakandare na wasu kwalejojin gwamnatin tarayya.

A cewarta ta yi wannan ƙarin bayani ne domin yin ƙarin haske kan kalaman Farfesa Owasanoye inda hukumar ta buƙaci jama'a da su yi watsi da rahoton da ke nuna cewa shugaban yana nufin tsarin ciyar da ɗaliban makarantun Firamare.

Me ma'aikatar ke cewa?

A wasu jerin sakonni da ta wallafa a Twitter, ma'aikatar ta nisanta ministar daga zargin wawure kudaden.

"Bayanan shugaban ICPC ba boyayye ba ne domin ya ce binciken wucin-gadi ya nuna an karkatar da naira biliyan 2.67 na ciyar da 'yan makaranta. Sannan akwai wani babban ma'aikacin gwamnati a ma'aikatar noma da ya karkatar da naira biliyan 2.5, koda yake ba a ambaci sunansa ba kuma an ce ya rasu, in ji ma'aikatar jin-kan.

Ta kara da cewa: "An yi wa kalaman shugaban hukumar ICPC gurguwar fahimta da fassara kuma ake neman alakanta wannan zargi da ma'aikatar jin-kai.

"Wannan kudin ciyar da daliban sakandaren da ake magana a kai ba shi da alaka da shirin ma'aikatar jin-kai na ciyarwa-Home Grown School Feeding- da ke karkashin Shirin tallafawa masu karamin karfi."

Ma'aikatar ta ce wannan shirin ciyarwar da ake zargin an karkatar da kudin na daliban da ke makarantun gwamnatin Tarayya ba karkashin ma'aikatar jin-kai ake gudanar da shi ba.

"Ma'aikatar Jinkai shirinta na yara ne 'yan firamare daga aji 1 zuwa 3 a wasu zababbun makarantun gwamnati a fadin kasar. Don haka babu sisin kobo da ke shigo mata ko take fitar wa kan wannan badakalar ciyarwar da ake zargin an karkatar da kudaden," a cewar sakon na Twitter.

Sannan batun naira biliyan 16 da ICPC ta ce ta gano a wata ma'aikata da su ma aka yi badakalarsu, sanarwar ta ce rashin adalci ne akan ma'aikatar jin-kai da minista Sadiya don haka take bukatar a gaggauta bankado sunayen mutanen da aka ce an gano kudaden sun shiga asusun su, kuma a rufe asusun ajiyar nasu, sannan mutane su yi watsi da labaran bogen da ake dangantawa da ma'aikatan jin-kai, a cewar sanarwar.

Me 'yan Twitter ke cewa?

Mutane da dama na sanya ayar tambaya kan yadda ake cewa an karkatar da wannan kudi, sannan suna neman karin bayanin ganin cewa wannan ba shi ne karon farko da ake fitowa ana irin wannan zargi ba.

Wasu kuma har yanzu na nuna rashin gamsuwa da martanin ma'aikatar jin-kai da minista Sadiya, inda suke cewa ita ma'aikatar ta bayyana sunayen makarantu firamaren da ta ce ta ciyar lokacin kullen korona.

Wani mai sharhi a Twitter, Abdul Mahmud, ya kalubalanci ministar inda ya ce: "Minista Sadiya, yanzu tun da kin tambayi ICPC ta bayyana sunan jami'in gwamnatin da ya almubazzarantar da N2.6B na ciyar da dalibai, ni ma a matsayina na dan kasa ina so ki bayyana mana sunayen makarantun da kika raba wa kudi a lokacin kullun korona."

Sannan akwai masu mika tambayoyi neman amsa ga gwamnatin Buhari kan salon yakin da yake da cin hanci da rashawa.

Abubakar A. Aliyu ya bayyana cewa: "Me kika ce? Yanzu an gano N2.67bn kudin ciyar da dalibai a asusun wasu mutane, a cewar ICPC. Da alama idan Shugaba Buhari ya gama mulki za a ce gwamnatinsa ta fi kowacce cin hanci. Abin da ya fi ban haushi shi ne idan mutum ya jawo hankalin Buhari a kan wannan batu ba zai damu ba."

Shi kuma Nazeefi ya ce: "An ciyar da gidaje 124,589 a Lagos, Ogun da Babban Birnin Tarayya a Shirin Ciyar da 'yan Makaranta tsakanin watan Mayu zuwa Yuli lokacin kunnen korona. Wannan shi ne karon farko da aka ciyar da mutane ta hanyar intanet a tarihi....'Yan damfara."

Karin haske

Wannan kudi da ake ce-ce-ku-ce a kan karkatar da su kusan wani dan kaso ne cikin kudaden da gwamnati ke cewa ta kashe wajen ciyar da dalibai a lokacin kullen korona.

Kafin wannan lokacin gwamnatin ta ce kimanin naira miliyan 523 da dubu 300 ta kashe kan shirin ciyarwa a makarantu lokacin kullen cutar korona.

Sadiya Faruƙ ta ce an kimanta kowanne zubin kwanon abinci a kan naira 4,200 bayan gudanar da cikakkiyar tuntuba.

Sannan a wannan lokaci, ta ce an tsayar da shawara kan yawan kudin ne daga kiyasin da hukumar kididdiga ta kasa da kuma babban bankin Najeriya suka samar.

Sadiya Faruƙ ta ce don tabbatar da ganin an yi komai cikin gaskiya da amana, sun hada gwiwa da Shirin Samar da Abinci na Duniya a matsayin kwararrun abokan aiki.

Baya ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irinsu EFCC da ICPC da hukumar tsaro ta DSS gami da wasu ƙungiyoyi don bin diddigin tsarin da ake gudanar da shirin.

Don haka bankado wannan badakala na karkatar da wani kaso cikin kudin ciyarwa a Najeriya abin daure kai ne, da ke sake jefa shaku a zukatan 'yan kasa.

Domin tun lokacin da aka fara batun ciyarwar mutane da dame ke tambayar yadda tsarin zai kasance la'akari da ganin cewa an rufe makarantu da dakatar da komai lokacin bullar korona, kuma har yanzu daliban ban da wadanda suka zana jarrabawar kammala makaranta da suka koma, zaman gida ake ci gaba da yi.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta