Aure a Zamfara: "Yadda na yi amfani da wani ɓangare na kuɗin auren 'yata na aurar da marayu 13"

Wani tsohon dan majalisar dattawa daga jihar Zamfara a Najeriya ya bayar da tallafin kayan daki ga wasu amare marayu su goma sha uku a garin Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.
Yanzu haka dai marayun da suka amfana da wannan tallafi baki har kunne saboda tagomashin kayan dakin da suka samu kyauta kasancewarsu marayu da har ma suka fitar da ran samun kayan dakin.
Tsohon dan majalisar dattawan, Sanata Kabiru Marafa, ya ce ya bayar da wannan tallafi ne bisa la'akari da yadda ake da yawan marayu a cikin jihar wadanda 'yan bindiga suka kashewa iyaye.
Tsohon sanatan ya ce: "A cikin jihar Zamfara a yanzu haka ba za a rasa marayu sama da dubu sittin zuwa dari ba, kuma wadannan marayu suna nan babu mai taimaka musu sai wanda ya dubi Allah ya ga ya dace ya yi wani abu."
Ya kara da cewa: "Da aka tashi auren 'yata, na yi mata nasiha a kan kada ta bari a yi mata almubazzaranci a bikinta akwai mabukata da za ta iya taimakawa da kudin da za ta yi wata hidima a bikin nata, kuma Alhamdulillah ta soke wasu bidi'o'i na bikin nata inda ta yi amfani da kudin nan har na taimaka wa wasu marayu goma sha uku da kayan daki."
Ya ce, akwai marayu da dama da aka sanyawa ranar aure, amma kuma saboda babu ya sanya ana ta daga bikin, wannan ne "ya sa na ga ya dace na zakulo wadanda aka jima da sanya ranar aurensu domin na musu kayan daki ko a samu a kawar da su."

An ɗaga biki sau tara saboda talauci

Asalin hoton, FACEBOOK
Sanata Marafa ya ce saboda rashi akwai yarinyar da aka ɗaga bikinta har sau tara, kuma idan aka yi la'akari da yadda bikin kauye yake dan abin da za a kashe bai taka kara ya karya ba, amma saboda maraici da rashi ana ta daga bikin.
Ya ce: "A kauyukanmu da naira dubu dari da hamsin za a iya yi wa yarinya kayan daki, amma kuma sai ka ga saboda rashi ana ta ɗaga biki, kuma al'ummarmu ba sa taimakawa irin wadannan marayun.
Wannan shi ne dalilina na yin wannan talalfi, kuma za a ci gaba da zakulo irin wadannan marayu ana taimaka musu, in ji sanata Marafa.
Iyalai da 'yan uwan wadanda suka samu wannan taimako sun ce babu abin da za su ce saboda yadda aka share musu hawaye ganin cewa sun kasa bikin 'ya'yansu saboda rashin kayan daki, amma gashi an yi wa 'ya'yan nasu kayan dakin.












