Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Operation Bamenda Clean: Abu biyar game da rundunar yaƙi da ƴan a waren Kamaru
A ranar 8 ga Satumba rundunar sojin Kamaru ta sanar da ƙaddamar da rundunar Bamenda da za ta kakkaɓe mayaƙa ƴan a ware daga ciki da wajen Bamenda.
Talakawa ne suka fi shan wahala a rikicin yankin renon Ingilishi wanda ya fara cikin lumana a 2016 daga baya ya rikiɗe ya koma yaƙi tsakanin ƴan a ware da dakarun gwamnati.
Lokacin da sojoji suka ƙaddamar da rundunar operation Bamenda Clean ta ce an ƙirƙire ta ne don kare al'umma, amma jama'a sun shigar da ƙorafi da dama ga hannun lauyoyi inda suka shigar da kokensu ga babban lauyan gwamnati na ƙasar kan yadda rikicin ke shafar jama'a.
Daga cikin ƙorafe-ƙorafen, an zargi jami'an tsaro da kama mutane har sai sun biya kuɗi kafin a sake su, kuma suna karɓar kuɗi da kuma yin kisan mutane da ɓalle kofar gidajen mutane ba tare da takardar kotu ba, kamar yadda Barista Mbah ya bayyana.
Mutanen Abakwa sun yi ƙorafin cewa jami'an tsaro na ɓalla kofa suna kama mutane, wasu sun ce suna shiga gidajen mutane suna tambayar takardar kayayyakin da suka gani a gidan har da katifa da wuka da adda, idan mutum ba ya da takardar shaidar kayayyakin da ya saya dole sai ya biya.
Amma ga abubuwan da ya kamata ku sani game da rundunar 'Operation Bamenda Clean'?
- Ƴan ƙasar na iya gabatar da ƙorafi ga rundunar sojin ƙasar idan har jami'an tsaro sun wuce gona da iri, ta hanyar tilasta musu biyan kuɗi. Kuma duk abin da suka karɓa, mutane za su iya kawo ƙararsu, kamar yadda Janar Nka Velera, shugaban rundunar soji a yankin arewa maso yammaci ya bayyana. Wasu da dama na tsoron shigar da ƙorafi domin suna ganin sojojin ke da wuka da nama.
- Jami'an tsaron da ke cikin rundunar suna da sharuɗɗa da suke bi da kuma ya kamata su kiyaye a duk lokacin da suka tafi bincike, kuma rundunar ta kunshi jandarma da ƴan sanda inda suke da littafiin da suke sa hannu da kuma sammacen zuwa binciken gidajen mutane. Ƴan ƙasar na iya tambayar sammacin.
- Ƴan ƙasar sai sun yi taka-tsantsan kan bayanan da suke samu domin wasu bayanan na ƙarya ne kan abubuwan da ake faɗa game da rundunar operation Bamenda Clean.
- Tun da jami'an tsaro ba su bayyana lokacin da za su yi samame, ya kamata kullum mutane su kasance cikin shiri, ka tanadi katin shaida, kuma ka buɗe ƙofa ga amsa tambayoyinsu cikin ruwan sanyi.
- Rundunar Operation Bamenda da ta fara aiki a ranar 8 ga Satumba babu lokacin kawo ƙarshen aikinta kuma za ta ci gaba da aiki har zuwa 1 ga Oktoba lokacin da mutanen yankin renon Ingilishi ke bikin samun ƴanci. Ya kamata ƴan ƙasar su yi taka-tsantsan kan yadda suke magana.