Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yarinyar da Whatsapp ya sada ta da danginta bayan shekara 20 da ɓata
- Marubuci, Daga Samba Cyuzuzo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Great Lakes
Wata yarinya da ta zama marainiya tana ƴar shekara biyu a lokacin kisan kiyashin Rwanda a 1994 yanzu ta gano wasu daga cikin danginta ta hanyar kafofin sadarwa na intanet.
Grace Umutoni, wadda ba ta san sunanta na asali ba, ta saka hotunanta da dama a shafukan sada zumunta na intanet irin su WhatsApp da Facebook da Twitter a watan Afirlu da nufin gano danginta, bayan ta kasa gano su a hanyoyi da dama.
Abu ɗaya da ma'aikaciyar jinyar mai shekara 28 ta sani game da asalinta shi ne an kawo ta ne a gidan marayu a Kigali daga garin Nyamirambo tare da ɗan uwanta, wanda ke shekara hudu a lokacin kafin daga baya ya rasu.
Akwai dubban yara kamar Mis Utomoni, da suka ɓata ko kuma aka raba su da iyayensu lokacin kisan kiyashi inda aka kashe sama da mutum 800,000 ƴan kaɓilar Tutsi da kuma wasu ƴan Hutus cikin kwana 100.
Da dama daga cikinsu suna binciken gano asalinsu - wani lokaci hakan yana da wahala saboda a bisa al'ada ba a kiran sunan mahaifi.
Bayan ta wallafa hotunanta, wasu mutane sun yi ikirarin cewa danginta ne - amma sai bayan watanni wani ya gabatar da kansa a matsayin ɗan uwanta.
Antoine Rugagi ya ga hotunanta da dama a WhatsApp kuma ya tuntuɓe ta ya ce tana kama sosai da ƴar uwarsa, Liliose Kamukama, wacce aka kashe a kwanakin farko na kisan kiyashi a watan Afrilun 1994.
'Abin da na yi ta fata'
"Lokacin da na gan shi, na fahimci muna kama da shi," Kamar yadda Umutoni ta shaida wa BBC game da mutumin da zai iya kasancewa kawunta.
"Amma gwajin DNA ne kawai zai tabbatar da ko muna da dangantaka da juna, kuma mun tafi mun yi a Kigali a watan Yuli."
Umutoni ta tafi kudancin Gakenke inda ta yi aiki da Mista Rugagi wanda ya zo daga garinsu a Gisenyi a yammaci, domin su karɓi sakamakon gwajin tare.
Hakan ya kasance babbar rana a gare su bayan gwajin ya nuna cewa suna da dangantaka da kashi 82.
"Na yi matuƙar mamaki, na kasa ɓoye farin cikina, ko a yau ina tunanin mafarki nake yi, wani abin mamaki ne da na daɗe ina addu'a a kai."
Kawunta da ta gano ya faɗa mata cewa sunan da iyayenta ƴan Tutsi suka raɗa mata shi ne Yvette Mumporeze.
Ya kuma yi ƙoƙarin gabatar da ita ga sauran dangi daga ɓangaren mahaifinta.
Waɗannan sun haɗa da gwaggonta da ta maƙale a Switzerland tsawon watanni saboda annobar korona.
Tun kafin sakamakon gwajin ya fito, har ta amince cewa Grace Umutoni ƴar yayanta ce bayan kwatanta hotonta da tsoffin hotunan dangi.
"Yarinyar ta tabbata ƴar ɗan uwana ce Aprice Jean Marie Vianney da matarsa Liliose Kamukama. Dukkaninsu an kashe su a lokacin kisan kiyashi."
'Mun yi tunanin ba wanda ya rayu'
Bucura ta faɗa mata asalin sunan ɗan uwanta cewa Yves Mucyo wanda aka kai su gidan marayu - Sunansa kawai ta iya tunawa - Sannan tana da ƙani ɗan shekara ɗaya da ake kira Fabrice.
An fara kisan kiyashi bayan jirgi ya ɗauki shugabannin Rwanda da Burundi - dukkaninsu ƴan Hutu - da aka harbo a daren 6 ga Afrilun 1994, daga nan aka fara kisan kiyashi a washegari.
Mayakan Hutu an faɗa musu su yi farautar ƴan Tutsi tsiraru - kuma yankin Nyamirambo a Kigali shi ne na farko da aka fara kai wa farmaki.
An kashe mutane, galibi da adduna, a cikin gidajensu ko a shingayen da aka kafa don duba waɗanda ke gudu - wasu sun yi ƙoƙarin ɓoye wa zuwa majami'u da masallatai a Nyamirambo a lokacin tashin hankalin.
Madam Bucura ta ce ta g lokacin da wani da makami ya ga wata mata ɗauke da Yves tana gudu - amma ba su san me ya faru ba. Babu wani bayani game da ƴar uwarsa.
An kawo ƙarshen kisan kiyashin a watan Yulin 1994 lokacin da ƴan tawayen Tutsi ƙarƙashin jagorancin shugaba na yanzu Paul Kagame, suka karɓi mulki.
"Mun yi tunanin babu wanda ya rayu, muna jimaminsu duk watan Afrilu duk shekara da ake tuna kisan kiyashi," a cewar Misis Bucura
Yayin da take girma, Mis Umutoni ba ta samu wasu ƙarin bayanai kan mutuwar Yves ba bayan sun isa gidan marayu.
Tana shekara huɗu wasu suka ɗauke ta daga gidan marayu inda a hannunsu ta girma ƴan kaɓilar Tutsi daga kudancin kasar waɗanda suka raɗa mata suna Grace Umutoni.
'Na girma cikin baƙin ciki'
A makaranta jami'ai sun taimaka min kuma sun koma gidan marayu a Kigali don tambayar ko akwai wani abu da suke da shi game da asalina, amma babu komi," in ji ta.
"Na rayu cikin baƙin ciki game da kasancewa wadda ba ta da asali, amma na ci gaba da yin addu'a."
"Duk da riƙe ni da kyau da waɗanda suka ɗauke ni suka yi, amma hakan bai hana ni dakatar da tunanin iyayena na asali ba, amma abu ɗaya game da ni da na riƙe shi ne sunan Yves da Nyamirambo - bayanan da ba su kai na soma bincike ba."
Ta damu ta san asalinta - kuma an shirya gagarumin bikin haɗuwa da danginta daga sassan Rwanda da sauran wurare, ko da yake annobar korona ta kawo tsaiku ga haɗuwar.
Amma duk da haka ana gabatar da ita ga dangi ta WhatsApp, kuma ta gano cewa tana da wani wanda suke uba ɗaya a Kigali.
Mahaifinta ya haife shi ne kafin ya yi aure.
'Mun gode wa iyayen da suka ɗauke ta.'
Tun 1995 kusan mutum 20,000 - yawancinsu yara ƙanana - ƙungiyar Red Cross ta haɗa su da iyayensu.
Muna samun buƙatu daga waɗanda suka tsira daga kisan kiyashin Rwanda waɗanda ke gidajen marayu," kamar yadda kakakinta a Rwanda Rachel Uwase ya shaida wa BBC.
Tun farkon 2020, ICRC ta haɗa mutum 99 da iyayensu waɗanda ba su san su ba tsawon shekaru 20.
Ga Misis Bucura, gano ƴar uwarta wani lokaci ne na godiya.
"Muna godiya ga waɗanda suka riƙe ta har suka ba ta suna," in ji ta.
Grace Umutoni ta ce za ta ci gaba da amfani da sunanta da waɗanda suka riƙe ta suka raɗa mata saboda da sunan ne aka fi saninta tsawon rayuwarta.
Amma ta gode wa kafofin sadarwa da suka taimaka wajen gano asalinta.
"Yanzu a kullum ina magana da dangina," in ji ta.
"Na shafe rayuwata ina tunanin cewa ba ni da asali."
Amma yanzu ina godiya ga dangina da suka ɗauke ni da kuma dangina na asali waɗanda dukkaninsu sun nuna min ƙauna."