Yadda ake zaɓen Sarki a Masarautar Zazzau

Mutuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ranar Lahadi bayan ya shafe shekara sama da 45 a kan karaga ta sa a yanzu hankali ya karkata ne ga wanda zai gaje shi.

A al'adance idan aka samu gurbi a masarauta sakamakon mutuwa ko wani dalili na daban, akwai tsarin da ake bi kafin a naɗa mutumin da zai kasance sabon sarki.

BBC ta tuntuɓi Shu'aibu Shehu Aliyu Daraktan gidan Tarihi na Arewa da ke ƙarƙashin Jami'ar Ahmadu Bello kuma a cewarsa idan Sarki ya rasu, akwai majalisar zaɓen sarki wadda ita ce take da alhakin zaɓar sarki.

"Yawanci an riƙa samun sauye-sauye tun kafin zuwan Turawa da kuma bayan zuwansu amma waɗanda suka zaɓi Sarkin Zazzau marigayi mutum biyar ne," in ji masanin.

A cewarsa, a duk lokacin da za a zabi sarki, gwamnati tana tura wakilinta zuwa ga majalisar zaɓen sarki wanda zai zauna da su domin tantance waɗanda suka nuna buƙatar zama sarki daga gidan sarauta guda huɗu -Gidan Katsinawa da Gidan Barebari da Gidan Sulluɓawa da Mallawa.

"Yawanci waɗannan gidaje suna zaɓen waɗansu su kan zaɓi wani daga cikinsu ya wakilce su, wasu kuma da kansu za su nuna buƙatar neman wannan sarauta amma mafi yawa gidajen sarautar sune suke nuna mutum ɗaya wanda zai wakilci wannan gida nasu a matsayin shi ne zai kasance ɗan takara wajen neman sarauta bayan sarki ya rasu." kamar yadda Shu'aibu Shehu Aliyu.

Hanyoyin da ake bi wajen naɗin sarki a Zazzau

Karanta ƙa'idoji

A cewar masanin, kafin majalisar ta zaɓi sarki, ana karantawa ƴan majalisar ƙa'idojin zaɓar wanda zai zama sarki da suka haɗa da:

  • Ya kasance bai taɓa yin laifi wanda hukuma ta kama shi ko ta hukunta shi ba.
  • Ya taɓa rike matsayi na sarauta ko hakimta a Zazzau
  • Samun cikakken ilimin zamani da na addini
  • Ya kasance ba mai yawan shekaru ba wato kada ya kasance tsoho tukuf
  • Tabbatar da cewa ya fito daga gidajen sarauta guda huɗu.

Ya bayyana wa BBC cewa a lokacin da aka zaɓi marigayi Dokta Shehu Idris, an yi amfani da waɗan nan ƙa'idoji.

Tantance sunaye a majalisar zaɓar sarki

Masanin ya ce bayan an karanto ƙa'idojin abu na gaba da ake yi shi ne tattaunawa kan yadda za a yi zaɓen - game da irin ayyukan mutanen da aka gabatar da su a matsayin wanda a cikinsu ne za a fitar da mutum ɗaya. Za kuma su duba ilimi da halayyar mutanen.

Bayan an tattauna ne kuma 'yan majalisar zaɓen sarkin suke zaɓar mutane uku daga cikin jerin mutanen da kowane gida ya gabatar kuma daga nan ne suke turawa gwamna sunayen mutanen ukun da suka yanke shawara a kai.

Aike wa gwamna sunayen

"Kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, zaɓen sarki a Zazzau ya ta'allaƙa ne a wuyan Sarkin musulmi a Sokoto - zai aiko da waziri shi kuma waziri shi ne zai yi ƙoƙari a cikin ƴaƴan sarki a zaɓi wanda za'a naɗa sarki, bayan zuwan turawan mulkin mallaka kuma zaɓen Sarki sai ya koma hannun gwamnan Lardin Arewa daga bisani ya koma hannun gwamnan jihar Kaduna." in ji masani Shu'aibu Shehu Aliyu.

Masanin ya ce an samu ƴan sauye-sauye a tsarin masarautu da gwamna ya yi a baya "bamu sani ba ko akwai wasu ƙa'idoji wanda gwamna zai ƙara fito da su wanda jama'a ba su san da su ba, wanda sun saɓa abin da aka sani."

A cewarsa, idan gwamna ya ga a cikin waɗanda 'yan majalisar sarki suka aike masa, yana da ikon ya ce a koma a sake tattaunawa domin zaɓar wasu wanda za su fi dacewa da ainihin tsarin da aka sa wanda alhakinsa ya ga an samu sarki ingantacce, salihi wanda jama'a za su gamsu da shi yana da ƙyawun ɗabi'u wanda jama'a za su amfana da shi.

Masanin ya ƙara da cewa, a cikin mutane uku da aka mikawa gwamna, gwamnan yana zaɓar mutum ɗaya wanda za a sanar a matsayin sarki.

Sanar da sabon sarki

Bayan gwamna ya fitar da sunan mutum ɗaya da ya ga ya dace ya zama sarki, gwamnati tana sanar da cewa an zaɓi sabon sarki a Zazzau.

"Daga bisani kuma sai a ba da sanarwa ga wanda shi ne sarki sannan sai a miƙa masa takardar cewa gwamnati ta zaɓe shi ya zama sabon sarki na masarautar Zazzau gaba ɗaya, bayan nan kuma za a zo a zauna a yi bikin miƙa masa babbar sanda ta masarauta." kamar yadda masanin ya sanar.

Bikin naɗin sabon sarki

Bayan sanar da sabon sarkin, ana shirya gagarumin bikin naɗin sarkin tare da mika masa takarda da kuma babbar sanda ta zama sarki na Masarautar Zazzau.

Ko akwai wani ƙalubale?

Masanin ya shaida wa BBC cewa a shekarun baya, mutane biyar ne suka haɗa majalisar zaɓar sarki - Waziri da Makama da limamin Kuna da limamin juma'a da Fagaci waɗanda sune suka naɗa marigayi Dokta Shehu Idris kan karagar sarauta.

Sai dai ya ce akwai mutum ɗaya da ya rasu cikin mutanen huɗun kuma har ya zuwa yanzu ba a kai ga naɗa magajinsa ba.

"Bamu sani ba shin za a yi ƙoƙari ne a ƙaro mutum ɗaya a samu mutum biyar ko kuma ya za a yi wanda shi ne ɗaya daga cikin babban ƙalubalen da zai fuskanci ainihin majalisar zaɓar sarki na sabon sarki a yanzu," in ji Shu'aibu Sheh Aliyu.