Rikicin Libya : Jagoran 'yan tawayen Libya ya amince da janye dakarunsa daga cibiyoyin mai

Asalin hoton, Jagoran 'yan tawayen Liibya
Jagoran 'yan ina da yakin Libya Janar Khalifa Haftar, ya ce a shirye ya ke ya cire shingen da ya sanyawa cibiyoyin samar da man fetur din kasar.
Ita dai gwamnati mai hamayya da ke mara masa baya ta mika takardar murabus a farkon wannan makon bayan zanga-zangar da aka yi a Benghazi da wasu birane kan tabarbarewar yanayin rayuwa da cin hanci da rashawa.
Janar Haftar ya ce sanarwar game da cire shingen man ta biyo bayan wata yarjejeniya da gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya a Tripoli wadda a karkashinta za a rarraba kudaden shiga na mai cikin adalci.
Wani Ministan gwamnati ya ce za a kafa wani kwamiti da zai kula da yadda ake shigo da kudaden.
Sai dai kamfanin mai na kasar ya ce ba zai ci gaba da aiki ba har sai sojojin Janar din sun bar cibiyoyin.
Shingen da ya sanya ya janyowa tattalin arzikin kasar gagarumin nakasu, abin da ya janyo asarar biliyoyin daloli.
Kafin daukar wannan mataki da yayi a watan Janairu, Libya na samar da man da yawansa ya kai ganga miliyan 1.2 a kowacce rana idan aka kwatanta da ganga dubu dari kacal da ake samarwa a yanzu.

Asalin hoton, Firai MInistan Libya Fayez al-Sarraj da Janar Khal
Kamar dai Syria, rikicin ya fara ne lokacin wani juyin juya hali da kasashen Larabawa suka yi a 2011.
Dakarun da ke samun goyon bayan kungiyar tsaro ta Nato sun hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekarar wadda tarihi ya nuna cewa shi ne ya fi dadewa kan karaga duk da fatan da ake samu a lokacin daga 'yan Libya da kuma kasashen duniya.
Tun lokacin, kasar take fuskantar yakin basasa.
Bayan shafe shekaru ana yaki, Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka wajen kafa gwamnati karkashin Firai Minista Serraj., gwamnatinsa karkashin jam'iyyar GNA da ke babban birnin Tripoli don hada kan kasar.
Ba kowa ne ya goyi bayan yarjejeniyar ba kuma Janar Haftar na son mulkar kasar.
Ya kafa dakarunsa LNA a gabashin kasar da ke da mazauni a biranen Tobruk da Benghazi, sannan ya yi ikirarin cewa shi kadai ne zai iya maido da tsaro tare da yakar rikicin masu da'awar kishin addinin Musulunci.
Dakarun Janar Haftar sun bazu zuwa birnin Tripoli tun Aprilun 2019, a wannan watan, sun yi yunkurin kwace iko da wani muhimmin birni mai suna Sirte.
Amma masu tada kayar baya suma sun kafa sansaninsu a birane daban-daban sannan wani reshen kungiyar IS suma suka bullo inda suke gudanar da harkokinsu a cikin dazuka.











