Rikicin Libiya: Abin da ya faru zuwa yanzu

Har yanzu rikicin Libya na cikin abubuwan da duniya ta maida hankali a kai inda kasashen duniya ke kokarin samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da suke sabani da juna.
A yanzu haka an samu baraka a gwamnatin kasar: daya mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya karkashin Firai Minista Fayez al-Serraj da kuma daya gwamnatin ta'yan tawaye karkashin Janar Khalifa Haftar.
Ko a makonnan, bangarorin biyu sun amince su tsagaita wuta bayan matsin lamba daga Rasha da Turkiyya.
Sia dai kamar yadda mutane da dama suka yi zato, lamarin bai tabbata ba saboda Janar Haftar ya ki amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar abin da ya kara jefa kasar cikin halin rashin tabbas.
Toh amma ta yaya lamura a kasar suka dagule haka?
Rashin cika alkawura

Asalin hoton, Getty Images
Yarjejeniyar da aka gabatar don tsagaita wutar rikicin da aka shafe watanni tara ana yi wanda ya samo asali tun da 'yan tawaye masu samun goyon bayan Janar Haftar suka fara kai hare hare.
Cikin watanni shida kadai, kimanin mutane 2,000 ne suka mutu wasu 146,000 kuma suka daidaita.
Jamus za ta karbi bakuncin wani taron tabbatar da zaman lafiya a Libya ranar 19 ga watan Janairu sai dai ba a san inda abubuwan da ke faruwa a baya-bayannan ba suke a taron.
Amma domin fahimtar dalilin da ya sa aka gaza cimma wata yarjejeniya, akwai bukatar mu san asalin yadda rikicin ya fara.
Game da Rikicin
Kamar dai Syria, rikicin ya fara ne lokacin wani juyin juya hali da kasashen Larabawa suka yi a 2011.
Dakarun da ke samun goyon bayan kungiyar Nato sun hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar wanda tarihi ya nuna cewa shi ne ya fi dadewa kan karaga duk da fatan da ake samu a lokacin daga 'yan Libya da kuma kasashen duniya.

Asalin hoton, Reuters
Tun lokacin, kasar take fuskantar yakin basasa.
Bayan shafe shekaru ana yaki, majalisar dinkin duniya ta taimaka wajen kafa gwamnati karkashin Firai Minista Serraj. Gwamnatinsa karkashin jam'iyyar GNA da ke babban birnin Tripoli don hada kan kasar.
Ba kowa ne ya goyi bayan yarjejeniyar ba kuma Janar Haftar na son mulkar kasar.
Ya kafa dakarunsa LNA a gabashin kasar da ke da mazauni a biranen Tobruk da Benghazi. Ya yi ikirarin cewa shi kadai ne zai iya maido da tsaro tare da yakar rikicin masu da'awar kishin addinin Musulunci.
Dakarun Janar Haftar sun bazu zuwa birnin Tripoli tun Aprilun 2019. A wannan watan, sun yi yunkurin kwace iko da wani muhimmin birni mai suna Sirte.
Amma masu tada kayar baya suma sun kafa sansaninsu a birane daban-daban sannan wani reshen kungiyar IS suma suka bullo inda suke gudanar da harkokinsu a cikin dazuka.
Yaki ba na kai-tsaye ba
Ga wani abu da ya sa rikicin ya yi kamanceceniya da na Syria: masu ruruta wutar rikicin Libya ba wai 'yan kasar bane kadai.
Duka bangarorin da ke rikici da juna a Libya sun samu kawaye daga yankin da ma kasashen duniya.

Asalin hoton, AFP
Hadaddiyar daular larabawa (UAE) da Saudiyya sun ce suna son fatattakar masu rikicin da'awar kishin Musulunci a yankin. Janar Haftar ya yi kokarin janyo kasashen garesa yadda ya bayyana kansa a matsayin makiyin masu tsaurin kishin addinin Musulunci.
Hadaddiyar daular Larabawa tare da Jordan sun samarwa dakarun LNA makamai da jiragen sama sannan wani rahoton majalisar dinkin duniya ya ce tallafin da UAE ke bai wa kasar ya taimaka wajen kashe farar hula a hare-haren da Janar Haftar ke kai wa.
Makwabciyar Libya, Masar na goyon bayan Janar Haftar sannan kuma ita ma ta ba shi tallafi.
Wataƙila wasu na iya cewa shugaban Masar Abdelfattah al-Sisi ya goyi bayan Janar Haftar, amma kuma Alkahira na ganin kwanciyar hankali ga Libya da hana rikice-rikice ko kuma masu tada kayar baya su bazu a kan iyakar kasar shi ne maslaha ga batun tsaron kasa.
Sannan ci gaba da kokarin ganin yin tasiri a yankin ya sa Rasha ita ma ta shiga cikin yakin. Wasu rahotanni na cewa sojojin Rasha na hada kai da dakarun Janar Haftar wajen yakin duk da Rashan ta musanta hannu a ciki.
Albarkatun kasa

Asalin hoton, Getty Images
A bangare guda akwai Turkiyya wadda ta aike dakarunta domin marawa Firai Minista Serraj baya.
Kamar Rasha, Turkiyya ita ma na son yin tasiri nan gaba sannan kuma a rika kallonta amatsayin babbar mai fada aji a yankin. Gwamnatin Turkiyya ta ce ta aike dakarun nata zuwa Tripoli kawai don horaswa da kuma bada shawarwari."
Amma wata majiya a gwamnatin GNA ta tabbatar wa BBC cewa aike dakaru da Turkiyya ta yi ya hada da 'yan tawayen Syria masu samun goyon bayanta.
A cewar rahotanni, manufar Turkiyyar ta aike dakarunta na da nasaba da samun dama ga albarkatun karkashin kasa masu daraja a kasar.

Sharhin Jonathan Marcus, wakilin tsaro na BBC:
A watan Nuwamba, Turkiyya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar raba teku da hukumomi a Tripoli abin da ya sa yankin da tattalin arzikin Turkiyya ke ikirarin shi kadai a yankin gabashin tekun Mediterranean.
An sha sukar wannan ikirarin amma matakin Turkiyyan wata alama ce ga sauran kasashen da suke da hannu a rikicin yankin abin da ya kara janyo kalubale wajen shimfida bututan iskar gas zuwa Turai har sai an sanya Turkiyya a batun.
Masu sharhi na ganin wani yunkuri ne na yakar Isra'ila da Masar da Girka da Cyprus wadanda suka kafa kungiyar iskar gas ta gabashin tekun Mediterranean.
Yadda Turkiyya ta sa kaimi wajen hako danyen mai a Cyprus ta hanyar amfani da jirage mara matuka.
Kasancewar Turkiyya a Libya na barazanar fadada rikicin a gabashin tekun Mediterranean da zai iya dagula alakar da ke tsakanisu da Rasha da kuma Amurka da kuma kawayensu na Nato.
Lamarin dai zai kara habaka rikici a yankin.
Turkiyya za ta yi fatan kasancewar dakarunta a Libya zai bata damar fadin ra'ayinta a duk sakamakon karshe da za a dauka.

Bukatar kasashen yankin
Qatar dai na ci gaba da takun saka da hadaddiyar daular larabawa da sauran kasashen yankin gulf a duk wani rikici a yankin sannan ta karkata ne ga gwamnatin da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya tare da kawarta Turkiyya.
Akwai kuma Faransa wadda ita ma take cikin rikicin na Libya tsundum tun 2015 da bukatun da suka shafi tattalin arziki da tsaro.
Faransa a hukumance ta ce tana goyon bayan gwamnatin Tripoli da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya sai dai ana zaton za ta goyi bayan Janar Haftar ba wai a siyasance ba har ma kan batun sojoji.
Italiya, wadda ta yiwa Libya mulkin mallaka a baya ta caccaki kusancin Faransa ga gwamnatin Haftar. Ta ce tana bayan Firai Minista Serraj wanda ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya.
Gwamnatin Italiya dai na da bukatar kashin kai kan daidaito a Libya saboda madakata ce ga bakin haure da ke kwarara yankin tun 2011.
Amurka ma tana cikin rikicin na Libya wadda ke yakar kungiyar IS a kudu maso yammacin kasar.
Me ya sa aka damu da batun?
Da alama akwai kasashe da dama da ke da hannu a rikicin na Linta kuma ga dalilin da ya sa suka damu.
Libya ce kasar da ta fi ma'ajiyar mai mafi girma a nahiyar Afirka sannan babbar mai samar da iskar gas ce.
Libya kuma hanya ce ga bakin haure ta isa Turai.
Sannan yadda IS da sauran kungiyoyin ta'addanci suka kafu abin tsoro ne ba wai ga kasashe makwabta ba.
Indai yakin Libya ya ci gaba, rikici na iya bazuwa zuwa wasu kasashen.










