Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rahama Sadau na shan yabo da suka bayan shekara bakwai a Kannywood
Masu bibiyar shafukanmu na sada zumunta da muhawara da ma wasu da ke bin diddigin rayuwar fitacciyar tauraruwar Kannywood, Rahama Sadau, sun bayyana ra'ayoyi mabambanta a daidai lokacin da take cika shekara bakwai tana harkokin fim.
A ranar Alhamis ne tauraruwar, wadda aka fi sani da Priyanka saboda kaunar da take yi wa tauraruwar fina-finan India Priyanka Chopra, ta sanar da cewa ta cika shekara bakwai tana fitowa a fina-finan Hausa.
A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Rahama Sadau, ta gode wa Allah bisa nasarorin da ta samu cikin shekara bakwai da ta yi tana fitowa a fina-finai.
Sakon yana dauke da hoton fim dinta na farko, Gani Ga Wane, wanda ta fito a matsayin budurwar Ali Nuhu kodayake wani dattijo a fim din, Shehu Hassan Kano, ya nuna cewa yana son aurenta.
Tun daga wancan fim din, Rahama ta fito a fina-finai masu dimbin yawa - na Hausa da na turanci da ake yi a Kudancin Najeriya.
Baya ga haka, ta dauki nauyin shirya fina-finai a kamfaninta na Sadau Movies, musamman fitaccen fim din nan na Mati A Zazzau da kuma Rariya.
Wasu daga cikin fina-finan su ne Jinin Jiki Na, Farin Dare, Wutar Gaba, Kasa Ta, Wata Tafiya, da Halacci.
Kazalika wasu daga cikin fina-finan turancin da ta fito sun hada da Sons of Caliphate, Up North, If I Am President, da Zero Hour.
Ra'ayoyin jama'a
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyi daban-daban a kan sakon da muka wallafa a shafukan sada zumuntar BBC Hausa a Facebook da Twitter da kuma Instagram inda muka nemi su gaya mana fim din tauraruwar da ya fi burge su.
A shafin Instagram, Khaleed Ringeem da Abba Mai Shadda sun ce sun fi son fim dinta na Kanwar Dubarudu.
Sai dai Bello Kadir Kad ya ce: "Ni fim din nata bai taba burge ni ba."
A shafin Twitter, @Laddon_Gusau ya ce ya fi son fim din Mati A Zazzau.
Su kuwa @ShapeeuBaddo da @Abdull_Azeezz sun ce sun fi son Matar Mutum.
A shafinmu na Facebook ma an samu ra'ayoyi daban-daban kan tauraruwar.
Real Journalist Mukhtar ya ce: "Fina-finanta da dama suna burge ni kuma jarumata ce sosai; yanzu ne dai na yi baya da ita bayan shigowar Maryam Yahaya."
Isah Kayarda ya ce: "Babu wata burgewa da ta yi, film dinta mafi yawa wulakanta tarbiyar addinin ce da al'adun mu, tunda take sana'ar film ba ruwanta da nuna mutuncin addininta, ballantana al'adar ta."
Sai dai ita kanta tauraruwar ta ce tana son dukkan fina-finanta.
A nasa bangaren, Barrister M. Runka addu'a ya yi mata yana mai cewa: "Ni a gaskiya na kasance daya daga cikin masoya Rahama Sadau sannan kuma a kodayaushe ina sa ta cikin addu'ata kamar yadda nake yi wa sauran 'yan uwana. Fatana a koyaushe Allah ya ba ta miji na gari ta yi aure kamar kowace mace."