Yadda sojin Najeriya suka yi dirar mikiya kan 'yan bindiga a Zamfara

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan bindiga da dama yayin wani hari ta sama da ta kaddamar kan maɓoyar 'yan bindigar da ke dajin Doumborou na jihar Zamfara.

Kwamanda Abdussalam Sani jami'i ne a hukumar da ke bayar da bayanai ta hukumar tsaron Najeriyar kuma ya shaida wa BBC cewa wadanda aka kashe din sun fito ne daga ɓangaren wani shahararren ɗan fashi.

A cewarsa, rundunar ta kai samamen ne ƙarƙashin Operation Wutar Daji na biyu a maɓoyarsu sannan an kashe da dama daga cikin 'yan bindigar.

Duk da ya ce babu ƙiyasin mutanen da suka kashe, suna ci gaba da bibiya don gano adadin mutanen da suka halaka.

"Ba a kama su ba amma an tarwatsa inda suke wato maɓoyarsu tare da inda suke ajiye makamansu. Ba mu gama bibiya ba amma idan Allah Ya yarda za a samu ƙarin bayani," in ji Kwamanda Abdussalam Sani.

A cewarsa, idan aka kai farmaki ta sama sojojin ƙasa za su yi bibiya domin samun bayanai na tafiye-tafiyen 'yan bindigar.

"Al'amura sun lafa a wannan daji kuma sojoji suna can suna bibiya," kamar yadda Kwamanda Abdussalam Sani ya bayyana.