Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump zai hana kayan China shiga Amurka saboda Musulmin Xianjiang
Amurka ta bawa hukumomin ta damar hana shiga da kayan da kanfunnan Chana da ke yankin Xianjiang.
Matakin karin matsin lamba ne kan muzgunawar da gwamnatin Chanar ke yiwa musulmin kabilar Uighur.
A cewar Amurka a na tursasa wa musulmin aiki don dole a wadannan ma'aikatu tamkar 'yan gidan yari.
Kayan da aka hana shigowa da su sun hada da sutura da kayan hada komfuta da makamantansu.
A na hasashen cewa Chana na tsare da musulmi sama da miliyan daya da suka fito daga yankin Xinjiang, inda ta kafa hujja da dalilan tsaro.
Kwamishinan hukumar fasakwauri ta Amurka Mark A. Morgan, ya ce matakin aikewa da sako ne ga kasashen duniya su fahimci cewa Amurka ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wurin kyamar bautar da al'umma.
Chana na noma kashi ashirin na audugar da ake fitarwa a kasuwannin duniya, kuma kaso mai yawa na audugar a na noma ta ne a yankin Xinjiang.