Yaushe ma'aikatan lafiya za su daina shiga yajin aiki?

Ma'aikatan lafiya sun ce gwamnati ta fifita likitoci fiye da su

Asalin hoton, @JohesuNigeria

Bayanan hoto, Ma'aikatan lafiya sun ce gwamnatin Najeriya ta fifita likitoci fiye da su

Yajin aikin ma'aikatan lafiya kamar ya zama ruwan dare a Najeriya, wanda ke tasiri sosai ga al'umma a asibitocin ƙasar.

A ranar Litinin ɗaya daga cikin manyan kungiyoyin ma'aikatan lafiya a Najeriya ta fara yajin aiki na tsawon mako guda kan kuɗaɗen albashi da inganta yanayin aiki.

Ƙungiyar da ta ƙunshi ma'aikatan jinya da masu binciken jini da masu bayar da magani na son gwamnati ne ta biya su kuɗaɗen da suke bi na albashi.

Yajin aikin na zuwa duka kwana guda bayan ƙungiyar likitoci ta janye nata yajin aikin a makon da ya gabata, ita ma game da waɗannan buƙatun.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana yajin aikin da gamayyar ƙungiyar ma'aikatan lafiya ta Joint Health Sector Unions (JOHESU) ta fara ranar Litinin a matsayin "karya doka".

Cikin wata sanarwa, Ministan Ƙwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce " yajin aikin bai dace ba kuma ba abu ne da ya zama dole ba."

Me ya sa ma'aikatan lafiya ke yawan shiga yajin aiki?

Ƙungiyar ma'aikatan kiwon lafiya na Najeriya ta ce yajin aikin da ta ke shiga na dole ne bayan sun bi duk hanyoyin da ya kamata amma babu biyan buƙata daga hukumomi.

Sakataren ƙungiyar Kwamred Silas Adamu ya shaida wa BBC cewa sun shafe lokaci suna bin gwamnati don ta biya buƙatunsu amma sai ta nuna ba ta damu da buƙatun ba.

Ya ce akwai tsarin albashi da aka sauya musamman da ya shafi ƙarin albashi na likitoci da kuma ma'aikatan lafiyar.

Amma a cewarsa suna ganin gwamnati ta fi kula da buƙatun likitoci fiye da bukatun ma'aikatan lafiya.

"Muna son gwamnati ta yi amfani da yarjejeniyar 2010 da aka amince, inda aka amince a yi wa ma'aikatan lafiya ƙarin albashi kamar yadda aka yi wa likitoci a tsarin.

"Muna son a gyara namu albashin kamar yadda aka yi wa likitoci," in ji shi.

Ya ƙara da cewa suna son kuma gwamnati ta biya su alawus dinsu da ta yi alkawali lokacin yaki da korona musamman alawus na hadarin aiki.

Sakataren ƙungiyar ma'aikatan na lafiya ya ce kashi 10 kawai gwamnati ta biya ma'aikatan lafiya daga cikin kudin alawus ɗin saɓanin likitoci.

Ma'aikatan kiwon lafiya sun taɓa shiga yajin aiki na tsawon mako shida a 2018 kan wasu buƙatun da suka ƙulla yarjejeniya da gwamnati waɗanda kuma ba a cika ba.

"Har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar ba," in ji Kwamred Silas

Ko za su dakatar da yajin aikin?

Yajin aikin ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya

Asalin hoton, @owawole

Bayanan hoto, Yajin aikin ma'aikatan lafiya na tasiri sosai ga al'umma a asibitoin Najeriya

Ƙungiyar ma'aikatan na lafiya ta ce yajin aikin na tsawon mako ɗaya, na gargaɗi ne kafin ta tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani.

Kuma yajin aikin ya shafi ma'aikatan asibitocin gwamnatin Tarayya ne a yanzu.

Ƙungiyar ma'aikatan lafiyar na Najeriya sun yi barazanar cewa idan har gwamnati ba ta diba buƙatunsu ba - za su zauna su yanke hukunci kuma akwai yiyuwar za su sake shiga yajin aikin kwanaki 15 kafin su tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani.

Gwamnatin Najeriya dai ta shawarci ƙungiyar ma'aikatan na Lafiya da ta sake tunani game da yajin aikin tana mai cewa - "Ba ya kan ƙa'ida gara a fifita mahimmancin lafiyar mutane fiye da komai".

JOHESU ta ɗauki matakin ne bayan kwamitin gudanarwarta na ƙasa ya yi wata ganawa ranar Asabar, inda ta ce ta fara yajin aikin daga 12:00 na daren Lahadi bayan ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin kwana 15 domin a biya mata buƙatunta amma "babu abin da aka yi".