Mali : Za a kafa gwamnatin rikon kwarya ta watannni 18

Gamayyar ƙungiyoyin 'yan adawa a Mali sun yi watsi da matakin da gwamnatin soji ta Mali ta ɗauka kan kafa gwamnatin riƙon ƙwarya na watanni 18.

A ranar Asabar ne sojojin suka bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin rikon kwaryar har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.

A baya dai sun bukaci a basu damar yin jagoranci har tsawon shekara biyu, sai dai da yake magana bayan tattaunawa ta kwanaki uku da 'yan hamayya da kungiyoyin fararen hula a Bamako, babban birnin kasar, wani kakakin su ya ce jami'in soja zai iya jagorantar gwamnatin rikon kwaryar.

Kungiyoyin 'yan adawar da shugabannin kasashen Afrika sun dage kan lallai ne shugaban ya kasance farar hula.

An kifar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ne a watan Agusta bayan zanga-zangar nuna fushi a kan yadda gwamnatinsa ta kasa kawo karshen matsalolin tattalin arziki da na masu ikirarin jihadi.

'Yan Mali sun yi na'am da juyin mulkin

Dubun dubatar mutane sun famtsama kan titunan Bamako babban birnin Mali domin yin murnar kawar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta yayin da ta tabbata ya yi adabo da kujerarsa.

Sojojin da suka yi juyin mulki sun kama Mr Keïta , suka tilasta masa ajiye mulki, lamarin da ya jawo musu allawadai daga fadin duniya.

Da ma Mr Keïta ya fuskanci tarzoma daga wurin 'yan kasar gabanin kama shi.

Dubun dubatar mutane sun taru a dandalin Independence da ke Bamako suna busa sarewa, inda wasu suka rika cewa sun yi nasara kan tsohon shugaban kasar.