Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Wanda aka yi wa gwajin riga-kwafin korona ya kamu da rashin lafiya
An dakatar da gwajin riga-kafin annobar Korona da kamfanin AstraZeneca da jami'ar Oxford da ke Birtaniya su ka samar, bayan da daya daga mutanen da ake gwaji kan su ya kamu da rashin lafiya.
Dama a na matakin karshe ne na gwajin, to amma dole ta sa a ka dakatar.
Kamfanin AstraZeneca ya bayyana cewa an dakatar da gwajin nan take saboda rashin fahimtar nau'in rashin lafiyar da ta kama wanda ake gwajin kansa.
An zuba ido sosai a fadin duniya don sanin sakamakon rigakafin annobar da AstraZeneca ta kuduri samarwa.
Rigakafin na hadin gwuiwa tsakanin kamfanin samar da maganin da jami'ar Oxford, shi ne a ka fi sa ran ya zama mafi inganci a cikin gwamman rigakafin da ake kan samarwa a fadin duniya.
Hakama riga-kafin ne aka zaci zai fara shiga kasuwa, don tuni ya tsallake matakan gwaji na daya da na biyu.
A yanzu ne ya shiga mataki na uku, inda ake gudanar da gwaji kan mutun 30,000 a Amurka da Burtaniya da kuma Afrika ta Kudu.