Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliyar ruwa: Yadda mata da yara suka nutse a kogi a Kebbi
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kebbi ta ce mata da kananan yara takwas ne aka tabbatar sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a kogi a karamar hukumar Jega.
Lamarin ya rutsa ne da matan da suka tashi daga ƙauyen Tungan Gaheru a ranar Litinin yayin da suke kan hanyar zuwa wajen wani biki a wani ƙauye da ke tsallaken kogi.
Matan sun nutse a ruwa ne yayin da suke kokarin hawa kwale-kwalen bayan an ajiye su a wani tsibiri sakamakon kaɗawar igiyar ruwa.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Kebbi Alhaji Sani Dododo ya shaida wa BBC cewa an cteo mata biyu, an kuma gawar mata uku, sannan ana neman gawar mace daya dayar uku.
Ya ce ana ci gaba da nemansu daga fadama zuwa fadama a hanyar da ruwan ke bi.
Yadda lamarin ya faru
Matan sun fita ne daga gidajensu tafiyar sada zumunci a wani ƙauye da ke tsallaken kogi domin taya farin ciki biki, to sai dai wani abin tausayi farin cikin na su ya koma baƙin ciki da jimami a duka garuwansu har ma da sauran faɗin jihar Kebbi.
Alhaji Sani Dododo ya ce lamarin ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi kusan dukkan faɗin jihar abin da ya sa koguna suka cika maƙil.
Ya ƙara da cewa matuƙin jirgin ya tsira sannan wasu mata biyu sun tsira daga hatsarin.
Abubukar Sani, shi ne matuƙin jirgin da ya kife da mutanen, kuma shi ya yi ƙoƙarin ceto biyu daga cikin matan da suke cikin jirgin, inda yana ji yana gani ya bar sauran matan suka nutse, domin babu yadda zai yi.
''Na saukar da su sun sauka sun hau tsibiri ni kuma na zagayo na wuce inda ruwan ya fi ƙarfi, na zagayo na zo don su hau, to a wajen hawan sai suka hau gaba ɗaya a lokaci guda, sai jirgin ya nutse.
''Na zuburo sai sauran suka rirriƙeni, na samu na kuɓutar da kaina, na kuma riƙo wasu biyu daga cikin matan da suka riƙe ni. To sai suka yi ƙoƙarin riƙo sauran ƴan uwansu da ke ta nutsewa.
''Da na ga haka sai na yi kururuwa mutane suka taho, aka yi ta ƙoƙari amma ina ba a samu ceto su ba,'' a cewar Abubakar.
Ya ƙara da cewa mutum 10 dama ya ɗebo cikin jirgin ciki har da yara. Amma takwas sun nutse a ruwan yayin da aka fiddo da biyu kawai.
Lamarin ya jefa jama'a da dama cikin halin rashin tabbas da kuma jiran tsammanin da Allah kaɗai ya san lokacin da zai yanke, musamman ga mutane kamar Malam Musa da matarsa da 'yarsa suka nutse a cikin ruwan.
Malam Musa ya shaida wa BBC cewa; ''ina kasuwa labari ya zo min, hankalina ya yi matuƙar tashi don tana ɗauke da goyon jaririyarta. Ina fatan Allah Ya gafarta musu ita da ɗiyata duka.''
Ya kuma ce an samu gawar matar tasa, ''sai dai gawar ɗiyar tamu da ta tafi da ita ne ba a gani ba,'' in ji shi.
Me ake ciki da batun neman sauran gawarwakin?
Hukummomi a jihar ta Kebbi dai sun ce tuni aka bazama neman gawarwakin sauran mutanen da ruwan ya ci.
Alhaji Sani Dododo ya ce: ''Daga wannan garin har zuwa Tungan Gehuru har Kimba har Jega, duk mun yi magana da shugabannin wajen ana duba gawarwakin.''
Ya ci gaba da cewa: ''Sannan mun nemi masunta da hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET, don gano su.
''Muna da yaƙinin za a samu gawarwakin don gawa ba ta nutsewa a ruwa, tana hayowa sama , sai dai kawai wataƙila a same su da nisa daga inda abin ya faru.
A yanzu dai lamarin ya zama na jira da sa ran ganin gawarwakin mutanen da suka nutse, a ƙalla iyalansu sa tabbatar da cewa an yi musu sutura kuma an yi musu ganin karshe.