Mace ta farko gwanar zamiyar kan ruwa a Senegal

Khadjou Sambe, mace ta farko gwanar zamiyar kan ruwa (Surfer) a Senegal, na gudanar da atisayenta a kusa da gidanta da ke yankin Ngor da ke birnin Dakar.

"Ina yawan ganin mutane na zamiyar kan ruwa, sai na fada wa kai na: 'Wai ina mata ne da suka iya zamiya?' a cewar Khadjou.

"Na yi tunanin: 'Me ya sa ba zan shiga zamiyar ba, na wakilci ƙasata, na wakilci nahiyar Afirka, da Senegal, a matsayar baƙar-fata?"

Ƴar Jaridar Reuters Zohra Bensemra ta adana hotunan atisayen zamiyar kan ruwa da Sambe da mutanen da take horarwa da ƴan mata da mata suka yi.

"Ina yawan tunanin kaina, Idan na tashi da safe: 'Khadjou, akwai abin da kika sa a gaba, kina wakiltar wani abu a ko ina a duniya, dole ki daina rufa-rufa, kar ki gajiya."

"Duk abin da mutane za su ce, kar ka saurare su, ka bi zaɓinka - saboda kowa ya tashi tsaye ya rungumi burinsa cewa za su iya zamiyar kan ruwa."

A yanzu gwanar tana jan hankulan masu tasowa domin karya alkadarin al'adu da rungumar zamiyar kan ruwa.

Sambe na horar da ƴan koyo a Black Girls Suf (BGS), makarantar horar da ƴan mata da mata da ke son gwanancewa a zamiya.

Tana ƙarfafa wa dalibanta gwiwar shiga ruwa da cire musu tsoro musamman a tsakanin al'umomin da suke tunanin zaman gida ne ya dace da su, su yi girki da goge-goge da aurar da su.

"Ina yawan shawartarsu da cewa su toshe kunnuwansu, su daina sauraron surutan mutane," a cewar Samba.

Sambe na alfahari da ƙabilar ta Lebou - ƙabilar da ke rayuwa a kusa da teku.

Ta taso a yankin bakin teku a birnin Dakar, Sambe ba ta taba ganin baƙar-mace na zamiya a kan tekun Atlantic ba.

A matsayinta na matashiya, iyayenta sun ƙi amincewa ta yi zamiya har na tsawon shekara biyu da rabi, wanda suka ce abin kunya ne ga zuri'arsu.

"Jajircewar da nayi ta tilasta musu sauya ra'ayi," a cewarta.

Sambe ta soma zamiyar kan ruwa tana da shekaru 14.

A tattaunwar ta da BBC, ta ce:"Lokacin da na soma gwada zamiya babu wani tsoro a tattare da ni, kawai ina cike da farin cikin shiga ruwa.

"Idan ka shiga tumbatsar farko, za ka ji wani irin farin ciki kamar ka yi ihu kowa ya ji ka - saboda ka cika burin shiga ruwa ka tsaya cir.

"Na farko da ɗan wahala saboda ni kaɗai ce mace da ke zamiya a nan, sannan mutane na ganin kamar: 'Me mace take yi a nan? Wannan wasan ai na maza ne.'

"A zahiri wannan zance ba gaskiya ba ne, sannan akwai sauran mutane da suka ƙarfafa mun gwiwa da fada min cewa kar na saurari kowa."

Mazaunan Ngor na yawan mamaki idan suka iske yadda Sambe ke rike allon zamiyar ta ta ratsa ta dan tsukukin hanyar da ke fitar da ita bakin teku.

Sambe tana atisaye tare da kociyarta Rhonda Harper (tsaye a hannun hagu), wadda ta kafa BGS.

Harper ta bayyana cewa Sambe ta iso babu ko sisi a jikinta, ba ta iya turanci ba sai dai kawai basira da hikimar da ke tattare da ita kan zamiya da kuma burin kafa kungiyar da zata kai ga nasara.

"Kamar ka yi ƙoƙarin fuskantar guguwa ne ka ɗaure igiya, saboda tana da hazaƙa da ƙwarewa ta musamman a harkar zamiya - da wuya samun irinta," a cewar Harper.

A ƴan watannin baya-baya nan, Sambe na tsaye daga gidanta tana hangen teku yayin da take atisaye.

"Idan ina kan ruwa, ina jin wani yanayi na ƙayatarwa sama da kowa, wani dadi na musamman ke mamaye zuciyata,'' a cewar Sambe.

Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka.