Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Ɗalibai fiye da 40 da ke rubata WAEC sun kamu da cutar
Ɗalibai fiye da arba'in da ke rubuta jarrabawar kammala sakandare ta WAEC sun kamu da cutar korona a Najeriya - akasari a jihohin Gombe da Bayelsa.
Hukumomi a jihar Bayelsa da ke kudancin ƙasar sun tabbatar da kamuwar aƙalla ɗalibai ashirin.
A Akwa Ibom kuma rahotanni na cewa ɗalibi daya ya kamu, yayin da a jihar Gombe da ke arewacin kasar ɗalibai ashirin suka kamu.
Kwamishinan Ilimi na Gombe, Dr Habu Dahiru, ya shaida wa BBC cewa an gudanar da gwaje-gwaje ga ɗalibai da malamai a makarantun kwana guda ashirin da ke jihar, kuma aka samu ɗalibai ashirin dauke da cutar a makarantu shida kawo yanzu.
''Ɗalibai sama da dubu muka yi wa wannan gwaji, kuma babu wanda za a je ba zai rubuta wannan jarrabawa ba saboda ya kamu da cutar.
Ɗaliban sun cigaba da daukan jarrabawar a gefe da kowacce makaranta ta ware domin killace duk wani ɗalibi da aka samu dauke da cutar.''
Dr Habu ya kuma kara da cewa akasarin ɗaliban basu nuna wata alamar cutar ba ko shiga yanayi mai tsanani, sannan akwai wayanda suka warke ma.
A makon jiya ne dai ɗalibai fiye da muliyan daya da dubu dari biyar suka fara rubuta jarrabawar ta WAEC bayan da aka jinkirta jarrabawar saboda tsoron yaduwar cutar ta korona.
Jarrabar WAEC tana da muhimmanci domin ita ke shirya yara samun damar shiga Jami'a da aikin yi.
Akwai dubban yara da ke irin wannan jarrabar a ƙasashe irin su Ghana da Saliyo da Gambia.