Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
WAEC: Yadda aka yi rabon tambayoyi da amsoshin jarabawar 2020 a sassan Najeriya
Takardar adabin Ingilishi ce ɗaliban da ke rubuta jarrabawar kammala sakandare za su rubuta a ranar Juma'a a ci gaba da jarrabawar Waec ta 2020 da ake yi.
Hukumar shirya jarrabawar Waec ta fallasa yadda wakilanta da masu kula da masu rubuta jarrabawar da kuma ɗalibai suka fitar da tambayoyi da amsoshin jarrabawar adabin Ingilishi tun kafin rubuta takardar.
A ranar 17 ga watan Agusta aka fara rubuta jarrabawar Waec a Najeriya amma kuma labarin shi ne yadda tambayoyin jarrabawar da dama ke ta yawo a kafofin sadarwa na Intanet lokacin da ɗaliban za su rubuta takardar lissafi da sauran fannonin ilimi da suka shafi kimiyya.
Saboda fayyace gaskiyar lamari kan wannan batu, hukumar Waec ta ce babu wata jarrabawar da aka fitar ko aka sata.
To ta yaya aka kwarmata jarrabawar?
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Waec Demianus Ojijeogu ya shaida wa BBC cewa wasu wakilanta da masu sa ido ga ɗaliban da ke jarrabawa ba su da kishin ƙasa, a wani lokaci ma ɗalibai na ɗaukar hoton takardar jarrabawar (wani lokacin ma ana cikin jarrabawar) sai su tura wa wasu da ke taimaka masu a waje.
Daga nan sai bayar da dukkanin amsoshin jarrabawar su tura wa ɗaliban ta hanyar wani shafin intanet, ko ta saƙon waya ko kuma ta kafar WhatsApp, wanda wannan ya saɓa wa dokar jarrabawar Waec; yin amfani da waya cikin ɗakin rubuta jarabawa.
Jami'in hukumar Waec a Najeriya ya ƙara da cewa akwai wasu bara gurbi da suka kama a jihohin Bauchi da Nasarawa da jihar Rivers da suke irin wannan aikin marar kyau na satar jarrabawa.
Jarrabawar adabin Ingilishi
Litattafai kamar Faceless - na Amma Darko da Piano and Drums - waƙe na Gabriel Okara da Birches - na Robert Frost Breakout da She Stoops to Conquer - wasan kwaikwayo na Oliver Goldsmith da Native Son - ƙagaggen labari na Richard Wright da Othello - na William Shakespeare da Harvest of Corruption - na Frank Ogodo Ogbeche suna daga cikin litattafan adabin Ingilishi na rubutun zube da Waec za ta tambayi ɗalibai tambayoyi a jarrabawar.
Wannan ne saƙon da hukumar Waec ta aika wa BBC Pidgin.