Juyin mulkin Mali: Abin da ya sa aka gaza cimma yarjejeniya kan gwamnatin riƙon-ƙwarya

Anasa ran za a ci gaba da tattanawa ranar Litinin

Asalin hoton, EPA

An kammala tattaunawa tsakanin masu shiga tsakani na yammacin Afrika da jagororin juyin mulkin Mali ba tare da cimma yarjejeniya kan gwamnatin riƙon ƙwarya ba, kamar yadda kakakin soji Kanar Ismael Wague ya shaida.

A wata sanarwa ta daban, ɓangarorin biyu sun ce shugaban da aka hamɓarar Ibrahim Boubacar Keïta - da sojoji ke tsare da shi tun bayan kifar da gwamnatinsa a makon da ya gabata - ba shi da niyyar dawowa kan mulki, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.

Shugabannin yammacin Afirka a baya sun bukaci a dawo da Keita kan mulkinsa, sai dai ana ci gaba da samun waɗanda suke nuna goyon-bayansu ga juyin mulki a Mali.

Tawagar masu shiga tsakani - ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan - zai mika rahotansa ga shugabannin yammacin Afirka kan ci gaban da aka samu.

Ƴan Mali ne za su yanke hukuncin karshe kan gwamnatin riko, a cewar Kanal Wague kamar yadda Reuters ta wallafa.

Me aka cimma tun farko?

Sai dai tun da fari wakilan kungiyar kasashen Yammacin Afirka, Ecowas, da mambobin rundunar sojin da ta yi juyin mulki a Mali sun amince da yarjejeniya kan batutuwa da dama, kwana guda bayan sun fara tattaunawa kan yadda kasar za ta koma kan turbar mulkin dimokradiyya.

"Mun samu damar cimma matsaya kan batutuwa da dama ko da yake ba mu cimma matsaya kan komai da komai ba," a cewar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda shi ne ke jagorantar sulhu tsakanin bangarorin biyu.

Bayanan bidiyo, Abubuwa biyar da da suka nuna cewa za a iya juyin mulki

Shugabannin sojoji sun bayar da shawarar kafa gwamnatin rikon kwarya ta sojoji wacce za ta kwashe shekara uku tana "duba ginshikan kasar ta Mali", a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP wanda ya ambato rahotanni daga wakilan Ecowas.

Shugabannin sojojin sun kuma amince su saki shugaban kasar da suka yi wa juyin mulki Ibrahim Boubacar Keïta, in ji AFP.

Ecowas ta nanata kiran mayar da Mr Keïta kan mulki.

Sai dai dubban 'yan kasar ta Mali sun fantsama kan titunan babban birnin kasar, Bamako, ranar Juma'a inda suka rika nuna goyon bayansu ga juyin mulkin.

Sun rika busa sarewa, inda wasu suka rika cewa sun yi nasara kan tsohon shugaban kasar.

"Ina matukar farin ciki, mun yi nasara. Mun zo nan ne domin mu gode wa dukkan jama'ar Mali saboda nasara ce ta jama'a," in ji Mariam Cissé, wani magoyin bayan 'yan hamayya, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

"IBK ya gaza," a cewar wani tsohon soja Ousmane Diallo.

Sai dai ya gargadi sojoji su bi a hankali, yana mai cewa "ya kamata soji su guji tunanin cewa sun zo ne su zauna a kan mulki".

Wannan layi ne

Ƙarƙashin matsi, jagororin juyin-mulkin na da mabambantan ra'ayi

Mary Harper, Editan Afirka, BBC World Service

Sojojin da suka ƙwace mulki a Mali sun ce suna tattaunawa da jam'iyyun adawa da sauran ƙungiyoyi a ƙoƙarin kafa gwamnati.

Duk da irin kiraye-kiraye masu ƙarfi daga shugabannin yankin Afirka da ƙetare kan dawo da shugaban da aka hamɓarar Ibrahim Boubacar Keïta kujerarsa, wadanda suka jagoranci juyin-mulkin da ƴan adawa sun nuna turjiya a baya amma yanzu da alama za a cimma matsaya.

Suna son mahukunta da za su iya yaƙar rashawa, farfado da tattalin arziki da kawo ƙarshen ƙabilanci da rikicin jihadi.

Abin ya zo da mamaki, musamman ganin yadda ƙasashe duniya suka gagara shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin siyasar ƙasar.

Presentational grey line