Kamuwa da Coronavirus: Shin ana iya samun cutar daga kwalin abinci na kanti?

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an samu cutar ƙwayar korona a wani kwali a kwanan nan a China na fuka-fukan kaji da aka shigo da su daga yankin kudancin Amurka.

Wannan ya sa ana ɗiga ayar tambaya kan ko cutar korona na yaɗuwa ta hanyar kayan abincin kwali.

Mene ne yiyuwar haka

Bisa ƙa'ida, akwai yiyuwar a kamu da cutar korona daga kayayyakin kanti.

Binciken da aka yi ya nuna cewa cutar korona na iya daɗewa tsawon sa'o'i ko kwanaki a kayayyakin kanti - yawanci a kantar ajiye kayayyakin da kuma ledojin da kayan ke ciki.

Haka kuma, cutar na iya tsayawa a wurin da babu zafi sosai, wanda kuma ana yawan sauya wa abinci muhalli.

Sai dai wasu masana kimiyya na nuna tababa kan ko za a iya hasashensu waɗannan sakamakon a ɗakin bincike.

Dakta Julian Tang, farfesan kimiyya a Jami'ar Leicester, ya ce yanayin muhalli yana sauyawa sosai, wanda ke nuna cutar ba za ta iya daɗewa ba.

Haka kuma Emanuel Goldman, farfesa a Jami'ar Rutgers, shi ma ya nuna cewa sakamakon ɗakin bincike kan yi amfani da samfuri na kwayoyin cuta miliyan 10.

A rubutun da ya yi a mujallar The Lancet: ya ce: "A ra'ayinsa, yiyuwar yaɗawa ta hanyar abin da ba shi da rai ba shi da yawa, kuma kawai sai a lokacin da wanda ya kamu da cutar ya yi tari ko atishawa ne a wurin sannan wani ya taba (tsakanin sa'a ɗaya zuwa biyu)."

Ya yaya cutar ke yaɗuwa?

Barazanar yaɗuwar cutar yawanci ya dogara ne da tunanin cewa ma'aikatan masana'antar hada abincin kanti za su iya taɓa wurin da aka ƴada cutar, daga nan su taba idanunsu ko hanci ko kuma baki.

Masana yanzu ba yarda cewa wannan ita ce hanyar yaɗa cutar ga yawancin waɗanda suka kamu ba.

"Zai iya yiyuwa mutum ya kamu da korona ta hanyar taɓa wurin da aka ƴaɗa cutar ko wani abu da yake ɗauke da cutar," kamar yadda hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Amurka CDC ta wallafa a shafinta na intanet.

Ta kuma ƙara da cewa wannan ba ita ba ce hanyar da cutar ta fi saurin yaɗuwa ba.

A zahiri, ta fi yaɗuwa kai-tsaye tsakanin mutum da mutum:

  • Mutane biyu da suka yi mu'amula zuwa (tsakanin minti biyu kuma tazarar ƙafa shida tsakaninsu)
  • ko ta hanyar wani ɗigon abu daga wanda ya kamu bayan ya yi tari ko atishawa ko yin magana
  • ko ɗigon ya shiga baki ko hanci kusa da mutane (wanda za a iya shaƙa zuwa cikin huhu)

Dakta Tang ya ce tabbatar da mutum zai iya kamuwa da kwayar cutar ta hanyar kayan kanti wani abu ne mai wahala.

Ta yaya zan kare kaina?

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce "babu wanda aka tabbatar ya kamu da cutar daga abinci ko wurin haɗa abincin." Amma ta bayyana matakan da ya kamata a bi don kauce wa kamuwa da cutar."

Ta ce: "Babu bukatar yin feshi ga kayan abinci, amma a dinga wanke hannu da kyau bayan kammala aikin haɗa kayan abincin na kanti da kuma kafin a ci."

Idan ka je sayayyar kayan marmari, ka yi amfani da man wanke hannu sosai kafin shiga kanti, kuma a wanke bayan ajiye kayan.

Kuma yana da kyau idan wanda zai kawo kayan a gida zai bi matakan kariya na lafiya da aka shata.

Yana da kyau a wanke hannaye da kyau bayan karbar kayan abinci daga waɗanda suka kawo, kuma masana sun bayar da shawarar yin amfani da leda sau ɗaya.