Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mamman Daura: Da gaske an garzaya da makusancin Shugaba Buhari Ingila? -
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 5
Sunan Mamman Daura ya kasance abin da ke yawo da jan hankali a shafukan sada zumunta a Najeriya bayan wayewar garin ranar Alhamis.
Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da rahotannin da ke yaɗuwa cewa ya yi bulaguro zuwa Landan domin ya ga likita.
Mamman Daura ɗan uwa ne kuma makusancin Shugaba Muhammadu Buhari da ake ganin yana da ƙarfin faɗa a ji a gwamnati, ko da yake ya musanta cewa yana yi wa sha'anin gwamnati katsalandan a wata tattaunawa da ya yi da BBC.
Da fari dai wasu jaridun Najeriya ne suka soma wallafa labarin da ke cewa an fitar da shi ƙasar waje saboda rashin lafiya.
Sai dai bayyanan da BBC ta samu daga iyalansa sun tabbatar da cewa ya tafi Landan din amma ba don ganin likita ba.
Wane halin yake ciki?
Majiyoyi daga iyalansa sun shaida cewa Malam Mamman ya yi wannan tafiyar ne tare da matarsa da kuma ɗaya daga cikin 'ya'yansa saboda ya samu hutu.
A cewar majiyar an jima tun kafin wannan lokaci ana son ya tafi turai domin ya huta amma yanayin dokar kulle ya dakatar da tafiyar.
Iyalan sun kuma ce ai ko a ranar Talatar da ta gabata ya je jana'izar tsohon dan jarida, Wada Maida.
Mece ce gaskiyar lafiyarsa?
Jita-jitar da ake yadawa sun ce Mamman Daura mai shekaru 79 an fitar da shi ne da jirgin kansa a ranar Laraba saboda matsalar numfashin da yake fama da ita tun ranar Juma'ar da ta gabata.
Wasu ma na danganta rashin lafiyar da cutar korona. Sai dai iyalansa sun tabbatar da cewa hutu ya tafi saboda ana yawan damunsa a gida. Sun kuma jadada cewa lafiyarsa ƙalau.
Amma jaridar Premium Times ta ambato wani aboki kuma makusancin Maman daura ɗin, Aminu Balele Kurfi, na cewa ya je duba lafiyarsa ne a London.
Aminu kurfi ya kuma shaida wa Jaridar cewa ''dama abokin nasa ya kan je Landan akai-akai domin tabbatar da lafiyar jikinsa''.
Me mutane ke cewa
Mamman Daura ya yi wannan tafiya ne duk da cewa ba a dage dokar korona kan haramcin shige da fice ta jiragen sama ba a Najeriya.
Don haka mutane da dama na ta ka-ce-na-ce a shafukan sada zumunta da ɗiga ayar tambaya kan yanayin aikin dokar ko akwai zaɓaɓɓun mutane da doka ba ta hau kansu ba.
Wani @Obong Ekpe a tuwita ya ce: ''Ya kamata a sani cewa an ɗage dokar jigilar jiragen sama na ƙasashen duniya ne jiya 19 ga Agusta maimakin 29 ga Agusta don kawai a bai wa Mamman Daura damar zuwa Burtaniya don ganin likita.
''Sannan ku tuna cewa kawuna shugaban APC ya mutu makonnin kaɗan da suka gabata kuma bai samu damar fita ƙasar waje don ganin likita ba.''
Ita kuwa @ayemojubar ta ributa: ''Aisha Buhari tana Dubai saboda ciwon wuya har yau shiru. Mamman Daura ya tafi Burtaniya don ganin likita.
''Wataƙila zuwa nan da 1 ga watan Satumba ogan da kansa zai tafi Burtaniya don ya je ya sha madara.''
Wasu kuma tsokaci suke kan jita-jitar da ke cewa rashin lafiya ce sanadiyar tafiyarsa kasar waje da kuma tabarbarewar fanin kiwon lafiyar kasar.
@Oluomoofderby ya ce: ''Babu wani ɗan siyasar Najeriya da ya je ƙasar waje ya dawo ya yi abin da ya gano a can na kirki a ƙasar nan.
''Buhari da Mamman Daura har ma da marigayi Abba Kyari duk sun je Burtaniya asibiti don ganin likita.'
''Ƴan siyasar Najeriya ba su da kunya.''
Wani @Deji_Bablo ya ce: ''Yawan kuɗin da ƴan siyasa ke kashewa a tafiya wasu ƙasashen neman magani zai iya isa a gina babban asibiti da duk kayayyakin aiki masu inganci da ake buƙata a Najeriya...''
Duk da cewa cikin dubban saƙonnin da aka wallafa a tuwita kan wannan batu mafi yawa na sukar Mamman Daura ne, mai magana da yawun Shugaba Buhari Garba Shehu ya kare bulaguron na Malam Mamman.
Ya ce dama ba a hana tafiya ba kawai dai jiragen ƙasashen ketare aka hana shigowa kasar.
Kullen korona
A ranar 23 ga watan maris Najeriya ta dakatar da sufurin jiragen sama da ciki da wajen kasar a cikin matakan data dauka na yaki da yaduwar annobar korona da yanzu haka ta kama 'yan kasar sama da dubu 50 da kashe 985
A ranar 8 ga watan yuli aka dawo da sufurin jirage na cikin gida, jiragen katare kuma ranar 29 ga watan Agusta ake saran su dawo da aiki.
Babu wani bayani mai gamsarwa kan dalilan da suka sa wannan doka ba tayi aiki a kan Malam Daura ba daya samu damar fita waje ana cikin wannan yanayi.
'Yan Najeriya da dama na ganin idan ma lafiyarsa zai duba ko ganin likita kamata ya yi a duba shi a kasar lura da halin da ake ciki na annoba.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya ce dama ba a hana tafiya ba kawai dai jiragen kasashen ketare aka hana shigowa kasar.
Sannan ya ce idan mutum yana da uzuri ko yana da jirginsa ko ya yi hayar jirgi shi kadai yana da damar fita yaje zuwa inda yake so.
Wannan kalamai na Garba Shehu ya tabbatar da zargi ko maganar da mutane key i cewa dama ana hada-hadar sufuri jirage musamman tsakanin masu hannu da shuni da wayanda ke cikin gwamnati.
Ko kafin wannan lokaci ma akwai rahotanni da suka tabbatar uwar gidan shugaban kasa da diyarta sun je Dubai.
Meyasa aka damu da Mamman Daura?
Malam Mamman wanda tamkar ɗa ne ga Shugaba Buhari, bayan ganin da ake masa na kallon mai ƙarfin faɗa aji da tasiri a harkokin gwamnatin Buhari.
Kalaman da ya yi baya-bayan nan kan batun tsarin karɓa-karɓa ne a mulkin Najeriya.
A cikin hirar Mamman Daura ya shawarci jam'iyyar APC mai mulki ta fifita cancanta kan la'akari da ɓangaranci wajen fitar da mutumin da zai gaji kujerar shugaban kasa bayan karewar wa'adin Buhari a 2023.
Kalaman na Mamman Daura ga dukkan alamu sun janyo ka-ce-na-ce cikin harkokin siyasar Najeriya, game da makomar shugabancinta bayan kammala wa'adin mutumin da ya fito daga yankin arewa.
Fadar shugaban Najeriya ta ce kalaman Malam Mamman Daura ba matsayin shugaban kasar ba ne ko na gwamnatinsa.
Wasu dai na ganin kalaman na Malam Mamman Daura tamkar hannunka mai sanda ne ga hasashen da wasu suka daɗe suna yi, amma fadar gwamnati ta kore wannan tunani.