'Fiye da shekara biyu ban ci abinci ba saboda larura'

    • Marubuci, Vitor Tavares
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • Lokacin karatu: Minti 3

"Me ke faruwa idan kika ci duk wani abu?"

Fernanda Martinez tana fama da tambayoyi kamar wannan a duk lokacin da ta buɗe shafukanta na sada zumunta.

Cikin tsananin juriya tana amsa su don bayyana yanayin larurarta ta gado da ba a saba gani ba, wadda a tsawon sama da shekara biyun da ta wuce ta sanya ta daina "cin abinci".

Matashiyar 'yar shekara 22 daga ƙasar Brazil tana fama da wani nau'in larurar da ake kira Ehlers-Danlos (EDS), wani rukunin larurori ne da ba a saba samunsu ba.

Suna dai janyo abubuwa kamar samar da sinadarin collagen ba a kan tsari ba ga jikin mutum - abin da kuma ke shafar yadda ɗan'adam ke narkar da abincin da ya ci.

Wannan larura tana da nau'i 13, kuma an yi ƙiyasi aƙalla duk ɗaya cikin mutum 5,000 a faɗin duniya yana fama da ita, a cewar Gidauniyar kula da masu larurar Ehlers-Danlos.

Sakamakon wannan larura, Fernanda ke rayuwa da kororon ɗura abinci tun a shekarar 2018 don kuwa jikinta ba ya iya narka abin da ta ci yadda ya kamata.

Ana kukan targaɗe kuma sai ga karaya, tana kuma fama da cutar kansa a maƙwallatonta, wannan larura ce da suka gada a cikin danginsu.

Sai dai Fernanda ta yanke shawarar cewa tana so duniya ta san wani abu game da larurarta don taimaka wa wasu don haka a kai a kai take wallafa bayanai game da batun a shafukan sada zumunta.

Babbar matsalar Fernanda a duniya ita ce cin abinci da abin sha, saboda in taƙaice muku bayani kawai ba ta iyawa.

Hanya guda kawai da take samun abinci mai gina jikin da take buƙata ita ce ta amfani da kororo don yi mata ɗure.

"Hanya ce da tamkar muna narka abincin ne a waje sannan mu haɗa wani ruwa mai cike da sinadaran amino acids da proteins da lipids da fats da glucose sannan a ɗura mata kai tsaye a jiki," ƙwararriya a fannin abinci mai gina jiki Pamela Richa, da ke raka Fernanda zuwa ganin likita ta bayyana.

Fernanda na alla-alla ta yi wa dubban ɗaruruwan masu bibiyar ta a shafukan sada zumunta ƙarin bayani kan yadda wannan abu ke aiki.

Kuma bayananta sun shahara. Bidiyon kyakkyawan fatanta da kalaman ƙarfafa gwiwa ga mutanen da su ma ke fama da irin waɗannan larurori sun samu yawan masu kallo sama da miliyan ɗaya a shafin TikTok.

"Tambayoyin ƙwaƙwa ba sa damu na kuma ina samun ɗumbin saƙwannin goyon baya daga mutanen da suka sauya yadda suke kallon rayuwata bayan sun ga irin jajricewata," Fernanda ta shaida wa BBC.

To taƙamaimai me yake damun Fernanda?

"Tun ina jaririya, Alamomi suka fara bayyana cewa wani abu a tare da ni ba daidai yake ba," in ji ta.

"Na taso lokacin yarinta da yawan jin zugi a ƙafafuwa da hannuwana. An haife ni da matsanancin tashin zuciya kuma kunnena ɗaya ya kurumce."

Tana kuma da murguɗaɗɗiyar mahaɗar gaɓɓai, abin da ke nufin tana iya juya gaɓoɓin jikinta fiye da misali, lamarin da cikin sauƙi kan haddasa cirar mahaɗa ko gocewarta.

"Waɗannan alamomi sun riƙa tsananta lokacin da nake ƙara girma... Kowa ya san akwai wani abu da ba daidai ba, amma taƙamaimai ba su san mene ne abin ba."

Sai ta hanyar kafar sada zumunta ne Fernanda ta samu taimakon warware abu da ya shige duhu, lokacin da ta gano wani zaure a Fezbuk da ke tattauna larurorin Ehlers-Danlos.

"Na je na samu ganin likitar ƙwayoyin halittun gado. Kuma ta yi dukkan gwaje-gwaje ta kuma tabbatar min da cewa ina da larurar," matashiyar ta ce.

Fernanda tana 'yar shekara 17 lokacin da aka gano larurar a jikinta.

Ya zuwa wannan lokaci yadda larurar ta taɓa lafiyarta, har abu ya ta'azzara.

Tuni har ta fara jin ciwon gaɓoɓi kuma tana fama da larurar sarewar jijiyoyin da ke daidaita aikin gaɓoɓi irinsu zuciyarta da 'ya'yan hanji, abin da ya sa suka daina aiki yadda ya kamata.

"Na riƙa fama da gudawa da amai da ciwon ciki," kamar yadda ta iya tunawa.

"To amma aƙalla duk abin da ke faruwa yana da suna. A yanzu na samu bayani kuma ina iya faɗa wa likitoci da sauran mutane abin da ke tare da ni."