Boko Haram: Gwamnonin Arewa na so a bai wa 'yan sanda makamai su tunkari kungiyar

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta kara azama a yaki da kungiyar Boko Haram a yankin.

Gwamnonin sun yi kiran ne yayin taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabas da ya gudana ranar Asabar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno Mallam Isah Gusau, ya shaidawa BBC cewa a yayin taron, gwamnonin sun cimma matsaya a kan batutuwa da dama, ciki har da bukatar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar da karin makamai na zamani ga sojojin da ke yaki da ayyukan ta'addanci a yankin.

Sannan sun bukaci a suma 'yan sanda a samar musu makamai na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin.

''Ko da yake gwamnonin sun yabawa kokarin gwamnatin Najeriya game da matakan da take dauka ta fuskar yaki da ta'addanci, sai dai sun ce akwai bukatar ta sake tashi tsaye domin kawo karshen wannan matsala'' in ji Isah Gusau.

Sun kuma zabi gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, domin zama shugaban kungiyar da zai jagorance ta har nan da shekaru biyu masu zuwa.

Karin wasu batutuwan da aka cimma matsaya a kansu yayin taron akwai maganar kammala dukkanin ayyukan hanyoyin da aka faro, kuma aka watsar ba tare da an kammala ba a yankin, da kuma bukatar ganin manoma sun samu damar yin noma, domin gudun fadawa halin yunwa.

Sannan gwamnonin sun bukaci gwamnatin Najeriya ta karfafa yunkurinta na gano man fetur a yankin da ta soma tuntuni, abin da suke ganin zai taimaka wajen samawa matasan yankin abin dogaro.

Kana sun cimma matsaya da shugabannuin hukumar kula da yankin arewa maso gabas da suma suka halarci taron, a kan su rika tuntubar jihohi a duk sa'ad da suke son gudanar da wani aiki domin kaucewa cin karon ayyuka tsakanin hukumar da kuma gwamnatocin jihohi.

An samar da kungiyar ne a watan Maris na shekarar 2020, domin tunkarar matsalolin da suka sha kan yankin, musamman matsalar tsaro.

Gwamnonin sun amince su mika shawarwarin da suka cimma ga fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin aiwatar da su a aikace.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hadar da mai masaukin baki, kana gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da kuma gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri, da gwamnan Bauchi Bala Muhammad Kaura, sai kuma gwamnonin Yobe da Taraba da suka tura wakilci.

Karin labarai da za ku so ku karanta: